Abokin tafiyar Atiku: PDP ta rage, tana duba hada Atiku da daya cikin wasu jiga-jigai 3
- Batutuwa na ci gaba da fitowa kan wanda ya kamata jam'iyyar PDP ta zaba a matsayin abokin gamin Atiku
- Makwanni da suka gabata ne jam'iyyar ta kammala zaben fidda gwani, ta zabi Atiku a matsayin mai rike da tutar jam'iyyar
- A yanzu, an kebe gwamnoni uku na yankin Kudu da ake sa ran za a zabi daya domin ya tafi da Atiku kafada da kafada
A yayin da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta kammala tantance abokin dan takararta na shugaban kasa, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, a yau, jam’iyyar na iya tunanin zabar dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023.
Bayan da Atiku ya samu tikitin tsayawa takara, ana sa ran zai fitar da dan takarar da zai samu karbuwa ga dukkan bangarorin kasar nan, wanda zai iya tattaro kuri'u daga yankin Arewa da Kudu.
A bangare guda, ana ci gaba da kai ruwa rana da kuma hasashen wanda ya fi cancanta ya yi wannan aiki ga jam'iyyar PDP.
Ba PDP kadai ba, haka labarin yake ga babbar jam'iyya mai mulkin kasar nan; jam'iyyar APC, inda ta ke ci gaba da tunanin mai gwabi da zai zama abokin tafiyar Bola Ahmad Tinubu da zai gwabza a zaben na 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya fi kusan sauki ga PDP, domin jam'iyyar APC ta shiga tarkon dogon tunani, kasancewa ana ta tada jijiyar wuya kan wanda ya kamata a zaba daga Arewa, tare da gujewa zabo musulmi ganin cewa Tinubu ma musulmi ne.
A jam’iyyar PDP kuwa, wata majiya da ke da kusanci da masu fada a ji a jam'iyyar ta shaida wa jaridar The Guardian cewa, an tsuke zabin wanda zai tafi da Atiku ga gwamnonin yankunan Kudu maso Gabas da Kudu-maso-Kudu da ke kan karaga a yanzu.
Adadin yawan gwamnonin PDP a yankin Kudu
Jam’iyyar na da gwamnoni tara a Kudu: Seyi Makinde (Oyo), Godwin Obaseki (Edo), Ifeanyi Okowa (Delta), Udom Emmanuel (Akwa Ibom), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), Nyesom Wike (Rivers), Douye Diri (Bayelsa). ), Udom Emmanuel (Akwa Ibom) da Okezie Ikpeazu (Abia).
Wasu daga cikinsu sun fito takarar shugaban kasa, inda aka kammala zaben fidda gwanin PDP kuma Atiku Abubakar ya lashe zaben kana ya karbi tikitin takara, gwamna Wike na Ribas ne ya zo na biyu a zaben.
Dan ba kara: Kuskuren PDP a zaben 2019, ba za a zabi laku-laku ba
Wata majiya ta shaida wa jaridar The Guardian cewa PDP ba ta son sake maimaita kuskuren 2019, inda ta zabi Peter Obi ya tafi da Atiku, wanda ya dade da barin kujerar gwamna, kuma suke takun saka da magajinsa, Willie Obiano.
Baya ga batun Obiano, farkon masu adawa da fitowar Obi a matsayin mataimakinsa daga gwamnonin Kudu maso Gabas ne, wadanda suka fito fili suka nuna adawa da waccan tikitin hadin gwiwa tare da kin goyon bayan da suka saba bai wa PDP.
A wannan karon, majiyar ta ce ana hango gwamnoni uku - Wike, Okowa da Emmanuel.
Baya ga Makinde da ke shirin kammala wa’adi na biyu, Diri wanda ke wa’adinsa na farko da kuma Obaseki, wanda shi ma har yanzu yana da karin lokaci a kan karagar mulki sauran gwamnonin yankin sun riga sun zabi zuwa majalisar dattawa, sun sayi tikitin sanata.
Wani takaitaccen bincike da aka yi ya nuna cewa Wike da Okowa na iya kasancewa a sahun gaba, inda Wike ke samun galaba duk da irin salonsa.
A duka dai, Wike da Okowa, jam'iyyar na fatan fansar bashin Kudu maso Gabas saboda su biyun 'yan kabilar Ibo ne kuma sun kwan biyu basu yi mulki ba.
Ka zabi daya: Shehu Sani ya tada kura a intanet, ya nemi Osinbajo ya zabi Atiki ko Tinubu
A wani labarin, Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar wakilai ta takwas, Shehu Sani, ya ce ya tambayi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya zabi dan takarar shugaban kasa kafin zuwan 2023.
Sani a wani sako da Legit.ng ta gani a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, 13 ga watan Yuni, ya ce ya roki Obasanjo ta Whatsapp da ya zabi dan takara tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Bola Ahmed Tinubu.
Tsohon sanatan ya kara da cewa zai yi wa mabiyansa bayani a dandalin sada zumunta idan tsohon shugaban kasar ya amsa masa.
Asali: Legit.ng