Sheikh Yahaya Jingir Ya Bayyana Hukuncin Deliget Da Suka Siyar da Kuri'unsu

Sheikh Yahaya Jingir Ya Bayyana Hukuncin Deliget Da Suka Siyar da Kuri'unsu

  • Fitaccen malamin addinin Islama na kungiyar Izala, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya sanar da matsayin deliget masu siyar da kuri'unsu
  • A cewar malamin, sun ci amanar jama'arsu tare da siyar da 'yancin al'ummarsu, wanda babu ko shakka sun halaka a addinance
  • Ya ce duk deliget din da ya siyar da kuri'asa ya siyar da kansa kamar yadda ya zo a a hadisin Annabi, ya halaka

Jos, Plateau - Shugaban majalisar malamai ta Jama'atu Izalatil Bidi'ah Wa Ikamatis sunnah ta Najeriya, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, yace duk wani deliget da ya siyar da kuri'arsa a wurin zaben fitar da gwani na 'yan takara, tabbas ya halaka.

Aminiya ta ruwaito cewa, Sheikh Jingir ya sanar da hakan ne a yayin da yake gabatar da wa'azi a Masallacin Juma'a da ke 'yan taya a garin Jos, jihar Filato.

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: Masu Ruwa da Tsakin APC Sun Magantu Kan Tikitin Musulmi da Musulmi

Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir a Masallaci
Sheikh Yahaya Jingir Ya Bayyana Hukuncin Deliget Da Suka Siyar da Kuri'unsu. Hoto daga aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

A cewarsa, abubuwan da masu takarar kujerun siyasa da deliget suka yi wurin amfani da kudi a wuraren zabukan fitar da gwani na 'yan takara da jam'iyyu suka yi abun kunya ne da bada tsoro.

Shehin malamin ya ce duk deliget da aka bai wa kudi domin siyan kuri'arsa ya kafa wa kansa mugun tarihi tare da siyar da 'yancin al'ummarsu. Ya ce daga deliget din har 'yan siyasan masu laifi ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Manzo Allah yana cewa, duk wanda ya siyar da kansa, ya halaka. Deliget an aike ku ne domin zabo mana shugabanni nagari, amma kun je an ba ku kudi kun siyar da 'yancin jama'a. Don haka babu abun da za ku zo ku fada wa mutanenku don kun ci amanarsu," yace.

Zaben Fidda Gwani: Akwai Babban Hatsari da ke Kunno kai, NWC ga Tinubu da Sauran 'yan takarar Kudu

Kara karanta wannan

2023: CAN ta Aike Sako ga Masu Neman Shugabancin Kasa, Ta Sanar da Irin 'Dan Takarar da Zata Zaba

A wani labari na daban, Shugaban matasan jami'iyyar APC na kasa, Dayo Israel ya ja kunnen 'yan takarar shugaban kasa da shugabannin siyasar kudu a kan rashin hadin kai.

Kamar yadda ya ce, akwai 'yan takarar shugaban kasa na kudu suna tsaka mai wuya a zaben fidda gwanin jam'iyyar da ake yi.

Israel ya bukaci 'yan takarar su girmama darajar gwamnonin arewa wajen mika mulki ga kudu. Daga cikin 'yan takarar kudu sun hada da jagoran APC na kasa, Bola Tinubu, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng