Burin Atiku a zaben 2023: Ina sa ran 'yan Najeriya za su yi kasa-kasa da jam'iyyar APC

Burin Atiku a zaben 2023: Ina sa ran 'yan Najeriya za su yi kasa-kasa da jam'iyyar APC

  • Atiku Abubakar, zababben dan takarar shugaba kasa a PDP ya bayyana bukatar yin waje da jam'iyyar APC
  • Ya bayyana haka ne bayan da dan takarar APC ya ce PDP ce silar dukkan wasu matsalolin da Najeriya ke fuskanta
  • Atiku ya yi magana mai kama da martani, inda ya ce jam'iyyar APC mai mulki ta tabbata ba ta tausayin 'yan kasar

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya koka da halin da kasar ke ciki, inda ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi waje da jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2023 mai zuwa.

Da yake nuna rashin jin dadinsa game da gazawar tsarin mulkin APC, Atiku ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su hada kai su tabbatar an kayar da APC a 2023 Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babban karramawar da za a yiwa jaruman damokradiyya shine fatattakar APC daga mulki – Atiku Abubakar

Atiku ya magantu kan batun zaben 2023
Burin Atiku a zaben 2023: Ina sa ran 'yan Najeriya za su yi kasa-kasa da jam'iyyar APC | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Ku tuna cewa dan takarar jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Sanata Bola Ahmed Tinubu, a makon da ya gabata ya aike da wani sakon murya kakkausar ga jam’iyyar PDP da ya ce kawai ta koma gefe ta shirya binne kanta a shekarar 2023.

Sai dai kuma a wani abin da ka iya zama martani, Atiku ta shafinsa na Facebook, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kasance a shirye don daukar mataki, inda ya lissafo wasu sassan da jam’iyya mai mulki ta gaza.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Leadership ta ba da rahoton rugujewar husumiyar wutar lantarki a baya-bayan nan da ta faru a kasar, wacce ita ce silar maganar Atiku a yau dinnan.

A cewarsa:

“Duhuwar da ta dabaibaye al’ummar kasar nan a cikin ‘yan kwanaki biyun da suka gabata na rugujewar da aka samu ta wuta, wani misali ne na rugujewar al’ummarmu: rugujewar hadin kai, rugujewar tsaro, durkushewar tattalin arziki, durkushewar ilimi, durkushewa rayuwa mai kyau -da rugujewar kimar rayuwa da mutuncin dan Adam.

Kara karanta wannan

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

“Abin da nake sa rai shi ne ‘yan Najeriya za su ruguza jam’iyyar APC mai mulki ta hanyar jefa kuri’a, su kuma daura tirba mai inganci a mulki domin kawo sabuwar Najeriyar burinmu da za ta kasance cikin hadin kai da kwanciyar hankali, wadata da mai cike da dama; amintacciya kuma hadaddiya. A dunkule waje daya, za mu iya yin hakan."

Bayan shan kaye a zaben fidda gwani, Osinbajo ya taya Tinubu murna

A wani labarin, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya taya jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu murnar nasarar da ya samu a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.

Richard Akinnola, mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Osinbajo ne ya taya Bola Tinubu murna, wanda ya lashe zaben kamar yadda rahotanni suka tabbatar, Business Day ta ruwaito.

Mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Yemi Osinbajo, a shafinsa na Facebook, ya ce: "Ina tayaka murna, Asiwaju Tinubu, wanda ake kyautata zaton ya lashe zaben fidda gwani.

Kara karanta wannan

Babu daga kafa: Duk da Atiku ya taya shi murna, Tinubu ya bayyana abin da zai yiwa PDP a zaben 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.