Ka kusa zama Jagaban Najeriya - Babagana Kingibe ya fada ma Tinubu cewa shine zai dare kan kujerar Buhari

Ka kusa zama Jagaban Najeriya - Babagana Kingibe ya fada ma Tinubu cewa shine zai dare kan kujerar Buhari

  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babagana Kingibe, ya karfafawa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, gwiwar cewa shine zai zama shugaban kasa na gaba
  • Kingibe ya bayyana cewa a yanzu ne Allah zai sakawa Tinubu kan dukkanin sadaukarwar da ya yiwa kasar
  • Ya kuma jadadda cewa dan takarar zai tashi daga Jagaban Borgu zuwa Jagaban Najeriya sannan daga Asiwaju na Lagas zuwa Asiwaju na Najeriya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babagana Kingibe, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Lagas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne shugaban kasar Najeriya na gaba, jaridar The Cable ta rahoto.

Tinubu dai shine ya yi nasarar lashe tikitin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a zaben fidda gwaninta da ya gudana a Eagle Square a ranar Laraba, 8 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

2023: Dalilin da Yasa APC ta Zabi Tinubu, El-Rufai Ya yi Bayani Mai Bada Mamaki

Jigon na APC ya samu kuri’u 1,271 wajen kayar da sauran abokan karawarsa su 13.

Ka kusa zama Jagaban Najeriya - Babagana Kingibe ya ba Tinubu tabbacin darewa kan kujerar Buhari a 2023
Ka kusa zama Jagaban Najeriya - Babagana Kingibe ya ba Tinubu tabbacin darewa kan kujerar Buhari a 2023 Hoto: The Cable
Asali: UGC

A yan kwanaki kafin zaben fidda gwanin na APC, Tinubu ya haddasa cece-kuce lokacin da ya ce shine ya kamata ya zama shugaban kasa na gaba saboda shi ya taimaki shugaban kasa Muhammadu Buhari har ya lashe zaben shugaban kasa na 2015.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun bayan da ya lashe tikitin shugaban kasar na APC, tsohon gwamnan na jihar Lagas yana ta ganawa da masu ruwa da tsaki don neman goyon bayansu gabannin babban zaben kasar mai zuwa.

Da yake jawabi a ganawarsa da Tinubu a karshen mako, Kingibe ya ce tsohon gwamnan na jihar Lagas ne zai zama shugaban kasa na gaba saboda sadaukarwarsa.

Da yake magana a taron Kingibe ya ce:

“Kai ne na gaba. Za ka tashi daga Jagaban Borgu zuwa Jagaban Najeriya; daga Asiwaju na Lagas zuwa Asiwaju na Najeriya. Saboda dukkanin sadaukarwa da ka yi, saboda dukkanin kokarin da ka yi, Allah zai saka maka a wannan lokacin.”

Kara karanta wannan

2023: Tinubu zai lallasa Atiku a Adamawa, in ji Babachir Lawal

Kingibe ya kasance abokin takarar MKO Abiola a zaben shugaban kasa na 1993, amma daga bisani ya yi aiki a karkashin gwamnatin soji na Sani Abacha bayan an soke zaben shugaban kasa na 12 ga watan Yuni.

2023: Yadda limamin Katolika ya fatattaki yan cocinsa da basu da katin zabe

A wani labarin, wani bidiyo ya bayyana kuma ya shahara a shafukan soshiyal midiya inda aka nuno wani limamin katolika yana umurtan mambobin cocinsa da basu da katin zabe da su koma gida.

Masu amfani da shafin twitter da dama sun wallafa bidiyon, ciki harda dan fafutukar siyasa, Rinu Oduala, wanda shine kan gaba wajen rijistan katin zabe.

Limamin Katolikan ya yi jawabi ga dandazon mabiyansa a gaban cocin, yana mai cewa kada wanda ya damu da zuwa coci cikinsu idan har basu da katin zabensu a hannu, Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng