Biyu Babu: INEC Tayi Watsi da Sunan Akpabio a Matsayin 'Dan Takarar Sanatan APC

Biyu Babu: INEC Tayi Watsi da Sunan Akpabio a Matsayin 'Dan Takarar Sanatan APC

  • Hukumar INEC ta yi watsi da Godswill Akpabio a matsayin 'dan takarar kujerar Sanata mai wakiltar arewa maso yamma na Akwa Ibom
  • Hukumar ta sanar da cewa ba ta san da sake zaben fidda gwani da APC ta yi ba a ranar Alhamis, Ekpo Udom ne ta sani 'dan takara
  • Kwamishinan zabe na jihar Akwa Ibom, ya ce tuni sun aike da suna tare da rahoton zaben fidda gwani da ya samar da DIG Ekpo Udom mai ritaya

Akwa Ibom - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta yi watsi da zaben fidda gwanin da ya samar da Godswill Akpabio a matsayin 'dan takarar kujerar sanata Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma karkashin jam'iyyar APC.

Akpabio, wanda ya janye daga takarar shugabancin kasa yace a zabi Tinubu a zaben fidda gwanin APC, an bayyana shi matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na kujerar sanatan Akwa Ibom a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

2023: Dalilin da Yasa APC ta Zabi Tinubu, El-Rufai Ya yi Bayani Mai Bada Mamaki

Biyu Babu: INEC Tayi Watsi da Sunan Akpabio a Matsayin 'Dan Takarar Sanatan APC
Biyu Babu: INEC Tayi Watsi da Sunan Akpabio a Matsayin 'Dan Takarar Sanatan APC
Asali: Original

Shugaban jam'iyyar APC na jihar, Stephen Ntukekpo, ya ce jam'iyyar ta umarcesa a mataki na kasa da ya sake zaben fidda gwanin sanatan sakamakon zargin magudi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kamar yadda sakamakon sake zaben ya nuna, Akpabio ya yi nasara inda ya samu kuri'u 478, yayin da DIG Ekpo Udom, wanda ya lashe zaben a farko, ya samu kuri'u uku kacal.

Amma a yayin jawabi ga Daily Trust a Uyo, babban birnin jihar a ranar Lahadi, REC din Akwa Ibom, Mike Igini, ya ce hukumar ta karba wanda yayi nasara ne a zaben da INEC ta lura da shi.

Ya musanta ikirarin cewa hukumar ta lura da sake zaben fidda gwanin, wanda Akpabio ya bayyana a matsayin mai nasara.

"An kammala zaben fidda gwanin a ranar 27 ga watan da ya gabata, don haka ban san abinda ku ke magana a kai ba. Wanda aka yi a baya shi ne wanda INEC ta lura da shi kuma tuni an aike da rahoton Abuja.

Kara karanta wannan

Bayan rasa tikitin gaje Buhari, gwamna ya karbe tikitin sanata na APC a hannun kaninsa

"INEC ba ta san wani zaben fidda na Sanata da aka yi a ranar Alhamis, 9 ga watan Yuni ba," yace.

Zaben fidda gwanin APC: Akpabio ya yi zazzafan martani game da janyewa daga tseren shugabancin kasa

A wani labari na daban, daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Godswill Akpabio, ya bayyana cewa ba zai janye daga tseren kujerar ba.

Hakan na zuwa ne yan awanni bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki sannan ya bukaci da su fito da dan takarar maslaha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng