Babban karramawar da za a yiwa jaruman damokradiyya shine fatattakar APC daga mulki – Atiku Abubakar

Babban karramawar da za a yiwa jaruman damokradiyya shine fatattakar APC daga mulki – Atiku Abubakar

  • Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bukaci yan Najeriya da su fatattaki jam’iyyar APC daga kan mulki a 2023
  • Atiku wanda ya nemi hakan a sakonsa na ranar Dimokradiyya ya ce ta wannan hanyar ne za a karrama jaruman dimokradiyya a kasar
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce gwamnatin APC mai mulki ta gaza cika manyan alkawaran da ta daukarwa yan kasar nan

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya yi kira ga yan Najeriya da su fatattaki jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga mulki a babban zaben 2023 mai zuwa.

Atiku ya yi wannan kira ne a ranar Lahadi, 12 ga watan Yuni, a cikin sakonsa na ranar dimokradiyya, yana mai cewa hakan shine babban abun da za a iya sakawa jaruman dimokradiyyan kasar da shi, Channels Tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Babu daga kafa: Duk da Atiku ya taya shi murna, Tinubu ya bayyana abin da zai yiwa PDP a zaben 2023

Babban karramawar da za a yiwa jaruman damokradiyya shine fatattakar APC daga mulki – Atiku Abubakar
Babban karramawar da za a yiwa jaruman damokradiyya shine fatattakar APC daga mulki – Atiku Abubakar Hoto: Thisdaylive
Asali: UGC

Dan siyasar ya yi imanin cewa wannan bukin lokaci ne da dukkan masu kishin kasa za su hadu domin yin tunani da kuma aiki tare don hadin kana kasar, tsaro, daidaito, ci gaban al’umma da tattalin arziki da kuma ci gaban kasar baki daya.

Ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan damar wajen karfafa jajircewarsu kan sadaukarwar da magabata suka yi wajen karbo yancin kan kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar tsohon mataimakin shugaban kasar, a bayyane yake cewa gwamnati mai ci ta kawowa al’ummar kasar gwamnati mafi muni.

Saboda haka, ya bukace su da su yi watsi da gwamnatin APC wacce ya bayyana a matsayin mara mutunci, mara farin jini, mara tunani kuma wacce bata san ya kamata ba.

Atiku ya jadadda cewa bai kamata a ba jam’iyyar da ta gaza cikawa mutane alkawaran da ta daukar masu game da tsaro, bunkasa tattalin arziki da yaki da rashawa damar sake yin wani wa’adi mara amfani ba.

Kara karanta wannan

Taron APC: Har yanzu Buhari bai zartar da hukunci kan mika mulki kudu ba - Badaru

A cewarsa, lokaci ya yi da za a tabbatarwa yan siyasar APC cewa da gaske mulki na mutane ne ta hanyar amfani da katin zabe.

A kullum ina rayuwa cikin bakin ciki da damuwa saboda matsalar tsaro - Buhari

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Lahadi, 12 ga watan Yuni, ya nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro a kasar Najeriya.

Buhari ya kuma roki yan Najeriya da su dage da addu’a a kan ranshin tsaro a cikin jawabinsa na ranar Damokradiyya ta 2022 da ya yiwa yan kasar a Abuja, jaridar Independent ta rahoto.

A cewarsa, gwamnatin na aiki tukuru domin magance matsalolin tsaro a kasar nan, jaridar The Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng