Atiku zai nemi hadin-kan Kwankwaso da Obi a 2023, APC na lissafin abokin takaran Tinubu
- Akwai yiwuwar Atiku Abubakar ya zauna da jam’iyyun NNPP da LP domin ya hada-kai da su
- Jam’iyyar PDP ta na tsoron Peter Obi da Rabiu su kawo mata matsala a zaben shugaban kasa
- Shi kuma Bola Tinubu yana tunanin yadda zai bi ya dauko wanda za su yi takara tare a APC
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - ‘Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa, Atiku Abubakar ya na tunanin zama da Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi a kan batun 2023.
Punch ta fitar da rahoto a ranar Asabar, 11 ga watan Yuni 2022 da ya bayyana cewa PDP za ta iya hada-kai da wadannan ‘yan takara biyu na jam’iyyan adawa.
Peter Obi ya yi wa Atiku Abubakar mataimaki da ya nemi takara a zaben 2019, a dalilin sabanin da ya samu da jagororin PDP ya sauya-sheka zuwa jam'iyyar LP.
Shi ma 'dan takaran NNPP, Rabiu Kwankwaso su na tare da Atiku Abubakar tare, daga baya dukkansu biyu suka samu kansu a APC, kafin su sake dawowa PDP.
PDP ta hango barazana
Masu hasashen siyasa su na ganin Sanata Kwankwaso da Obi za su iya gwagwuyewa PDP kuri’u da jam’iyyunsu na NNPP da LP a yankin Arewa da na Kudu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Saboda haka ne jaridar ta ce PDP ta na tunanin hada-kai da su domin a doke Asiwaju Bola Tinubu.
Paul Ibe ya shaidawa jaridar cewa Atiku Abubakar yana ta kokarin ganin yadda za a samu nasara, amma bai da labarin an kai ga tuntubar Obi da Kwankwaso.
Darekta Janar na kwamitin yakin neman zaben Peter Obi, Dr Doyin Okupe, ya tabbatar da cewa ‘dan takararsu ba zai karbi tayin janyewa wani ‘dan takara ba.
Tinubu yana ta lissafi
A jam’iyyar APC kuwa, ana ta tunanin wanda za a dauka domin ya yi wa Asiwaju Bola Tinubu takarar mataimakin shugaban kasa a zaben da za ayi a 2023.
An fara tunanin daukar Gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong ko Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, wanda dukkaninsu kiristocin Arewa ne.
Simon Bako Lalong shi ne shugaban gwamnonin Arewacin Najeriya, sau biyu yana lashe zabe a APC. A 2023 zai bar mulki, har ya samu takarar kujerar Sanata.
Shi kuwa Boss Mustapha mutumin jihar Adamawa ne wanda tun 1992 ya shiga siyasa. Boss ya zama sakataren gwamnati ne bayan an tsige Babachir Lawan.
A ranar Juma'a aka ji tabbatar da cewa Jita-jitar neman takarar Goodluck Jonathan a 2023 ta kare. An yi rade-radin Jonathan zai sake neman shugabanci.
Tsohon shugaban kasar ya taya Atiku Abubakar, Bola Tinubu, Peter Obi da su Rabiu Kwankwaso murnar samun takara a zabe mai zuwa, ya kuma yi kira gare su.
Asali: Legit.ng