2023: Jam'iyyar PDP Ta Bayyana Lokacin Da Za Ta Sanar Da Wanda Zai Yi Wa Atiku Mataimaki
- Babban jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta kwafa kwamiti na musamman da za ta yi aikin zabo wanda zai yi wa Atiku Abubakar mataimaki a zaben 2023
- Ologunagba, mai magana da yawun jam'iyyar na PDP ya tabbatar da kafa kwamitin yana mai cewa mako mai zuwa za su sanar da mataimakin Atiku idan an kammala tuntuba
- Kakakin na jam'iyyar PDP ya ce ana tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki wurin zabo wanda zai yi wa Atikun mataimakin shugaban kasa amma bai ambaci sunan yan kwamitin ba
Jam'iyyar APC da PDP, a ranar Alhamis sun bada himma wurin neman wadanda za su yi wa yan takarar shugabannin kasarsu mataimaki.
PDP ta kafa kwamiti wanda ya kunshi gwamnoninta, kwamitin ayyuka da kwamitin amintattu da tsaffin gwamnoni don zabo wanda zai yi wa jam'iyyar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023.
Kwamitin ta yi taro a ranar Laraba da Alhamis a Abuja. Kakakin PDP, Debo Ologunaba, ya tabbatar wa The Punch kafa kwamitin a daren ranar Alhamis.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An tattaro cewa Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike da takwararsa na Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, sun dage suna ta bin kafa wurin masu ruwa da tsaki a PDP don ganin su aka zaba.
A bangarensa, dan takarar shugaban APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis, shima ya fara neman wanda zai masa mataimaki a taron da ya yi da gwamnonin arewa.
Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta umurci jam'iyyun siyasa su mika mata sunan yan takararsu da mataimaki kafin ko ranar 17 ga watan Yuni.
The Punch ta rahoto cewa a ranar Alhamis, Atiku ya gana da wasu gwamnonin jam'iyyar PDP a yunkurinta na zabo masa mataimaki.
Za mu sanar da mataimakin Atiku mako mai zuwa idan mun kammala tuntuba, Ologunagba
Ologunagba a hirar da ya yi da The Punch, ya nuna cewa PDP za ta sanar da dan takarar mataimakin shugaban kasarta a mako mai zuwa.
Amma, ya ki ambatar sunan wadanda ake duba yiwuwar zabo mataimakin daga cikinsu.
Ya ce:
"Eh, mun kafa kwamiti don nemo mataimaki, idan sun cimma matsaya, za mu sanar. Ba hasashe muke yi ba. Akwai tsari, ba mu aiki ba tare da tsari ba. Muna bin doka, muna tuntuba, shine abin da muke yi.
"Idan mun gama tuntuba, za ka ji sakamako. Ko sun yi taro yau Alhamis ko ba su yi ba, bai da muhimmanci. Idan sun gama aikinsu za ka ji sakamako."
Da aka tambaye shi sunayen yan kwamitin, Ologunagba ya ce, "Ba ka bukatar sunayensu. Dukkan bangarorin jam'iyyar mu suna da wakilai, Kungiyar gwamnoni, Kwamitin Ayyuka, Kwamitin Amintattu, da tsaffin gwamnoni. Ana tuntubar dukkan bangarorin masu ruwa da tsaki da ya dace."
A kan batun sasanta wadanda suka sha kaye yayin zabin fidda gwani, ya ce jam'iyyar na aiki don yin sulhu tsakaninsu.
Asali: Legit.ng