2023: A karon farko, Bola Tinubu ya tabo magana game da wanda zai zama Mataimakinsa

2023: A karon farko, Bola Tinubu ya tabo magana game da wanda zai zama Mataimakinsa

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyara ta musamman zuwa fadar Shugaban na Aso Rock Villa
  • An tambayi ‘Dan takarar shugaban kasan na 2023 a game da wanda za su yi takara da shi a APC
  • Tinubu ya ki amsa wannan tambaya, ya ce a yanzu ba zai fadawa kowa wanda za su raba tikiti tare ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda zai yi wa jam’iyyar APC mai mulki takarar shugaban kasa ya yi magana a kan zabin mataimakinsa a 2023.

Daily Trust ta ce Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya tabo wannan batu ne a lokacin da ya ziyarci Mai girma Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa a Abuja.

Da yake yi wa manema labarai jawabi a ranar Alhamis, Bola Tinubu ya yabi Muhammadu Buhari na bada dama ga duk wanda ya iya allonsa ya wanke.

Kara karanta wannan

Barazana da kalubale 8 da Bola Tinubu ya fuskanta wajen zama ‘Dan takaran APC a 2023

‘Dan takaran ya ce shugaban kasa ya cika alkawarin da ya yi na cewa zai goyi bayan adalci wajen fito da ‘dan takarar shugaban kasa, kuma haka aka yi.

Buhari ya cika alkawari - Tinubu

“Ya yi wa duk kasar nan alkawari zai bar tarihin gaskiya; zai bada dama ga ‘yan takara su nemi mukami. Ya ce zai tabbatar da damukaradiyya, kuma ya yi hakan.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Bola Tinubu

Jaridar ta rahoto Tinubu yana cewa ba nasararsa ce ke da muhimmanci ba, sai dai hanyar da aka bi wajen fito da ‘dan takara ba tare da an nuna fifiko ba.

Bola Tinubu
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock Villa Hoto: Mr_JAGs
Asali: Twitter

Da me Tinubu zai yi talla?

‘Yan jarida sun nemi jin ko Bola Tinubu yana da abin da zai tallatawa masu zabe, ya kuwa ce akwai. Tinubu ya ce zai dora daga inda Buhari ya tsaya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya mamayi Farfesa Osinbajo, ya kai masa ziyara kwatsam har ofishinsa a Aso Villa

“Ina da basira, na kware a aiki daga aikin da nayi a kamfanoni masu zaman kansu da gwamnati, kuma a shirye nake in fara aiki ba tare da bata lokaci ba.”
“Ba zan lalata ayyuka da gaskiyar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, ya mika mani ba.”

- Bola Tinubu

"Ba zan fada maku ba"

Da aka tambayi Tinubu ko wa zai zama abokin takararsa, sai ya nuna cewa wannan sirri ne da ya birne a kasan zuciyarsa, kuma ba zai sanar da kowa a yanzu ba.

"Ba zan fada maku wannan ba. Wannan hakki na ne; yana boye cikin 'dan karamin littafi na."

Jonathan ya yi kira ga Tinubu da su Atiku

Ku na da labari jita-jitar neman takarar Goodluck Jonathan ta kare, har ya taya Atiku Abubakar da su Asiwaju Bola Tinubu murnar samun takara a zabe mai zuwa.

Tsohon shugaban kasar ya fara da PDP da sauran wadanda aka ba tuta, ya nuna masu muhimmancin tabbatar da zaman lafiya da neman mulki cikin tsabta.

Kara karanta wannan

Zaben APC: Yadda Gwamnoni, Jagororin Arewa da ‘Yan NWC suka ba Bola Tinubu nasara

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng