Hudubar da Goodluck Jonathan ya yi wa Atiku, Tinubu, Obi, Kwankwaso da suka samu takara

Hudubar da Goodluck Jonathan ya yi wa Atiku, Tinubu, Obi, Kwankwaso da suka samu takara

  • Goodluck Jonathan ya ba ‘yan takarar shugaban Najeriya a 2023 shawarar su yi kamfe mai tsabta
  • Tsohon shugaban na Najeriya ya taya Atiku, Tinubu, Obi da su Kwankwaso murnar samun takara
  • Dr. Goodluck Jonathan ya bukaci masu ruwa da tsaki su maida hankali a kan zaman lafiyan kasa

Abuja - Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi kira ga masu takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023 da su guji raba kan al’umma.

Dr. Goodluck Jonathan ya yi wannan kira ne a jawabin da ya fitar a shafinsa na Twitter, yana mai taya wadanda suka samu takara murnar lashe zaben gwani.

Da yake magana a ranar Alhamis, 9 ga watan Yuni 2022, tsohon shugaban na Najeriya ya ce akwai bukatar a gujewa kazamin kamfen domin a cigaba.

Kara karanta wannan

Zaben APC: Yadda Gwamnoni, Jagororin Arewa da ‘Yan NWC suka ba Bola Tinubu nasara

“Ina taya wadanda suka yi nasara a zabukan fitar da gwani a jam’iyyun siyasa musamman Alhaji Atiku Abubakar, ‘dan takarar jam’iyyar PDP, Peter Obi na jam’iyyar LP, Asiwaju Bola Tinubu wanda ya yi nasara a APC da sauran jam’iyyun da suka kammala zaben fitar da gwani.”
“Wadannan sun hada da Sanata Rabiu Kwankwaso a NNPP, Malik Ado-Ibrahim a YPP, Cif Dan Nwanyanwu a ZLP, Dumebi Kachikwu a ADC da Adewole Adebayo na jam’iyyar SDP.”

- Goodluck Jonathan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Goodluck Jonathan
Goodluck Jonathan tare da Atiku Abubakar Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jonathan ya tunawa masu takaran cewa an tsaida su ne bayan an kai-an komo a jam’iyyun.

Kamar yadda Punch ta fitar da rahoto, Jonathan ya ce wadanda aka ba tikiti sun yi imani da tsarin farar hula, don haka suke neman kawo cigaba a kasar.

Ayi kamfe mai tsabta - Jonathan

“Yayin da za ku shiga yakin neman zabe, akwai muhimmancin maida hankali wajen tunkarar abubuwan da suka shafi kasar nan, tare da kawo mafita.”

Kara karanta wannan

PDP tayi magana a kan 2023, ta yi hasashen yadda za ta kare tsakanin Atiku da Tinubu

“Ina mai kira a gare ku da ku yi kamfe mai tsabta, a guji raba kai da cin amana, ta yadda a karshe Najeriya za ta yi nasara, damukaradiyya zai yi galaba.”

- Goodluck Jonathan

A tsare rayukan jama'a

Har ila yau, Jonathan ya ce dole ne ‘yan takara su guji rigima da duk abin da zai yi sanadiyyar zubar da jini ta hanyar kiyaye irin maganganun da za su rika yi.

Jonathan ya yabawa yadda wadanda suka sha kashi a zabukan, suka rungumi kaddara, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da matasa su dage a samu zaman lafiya.

Za mu doke Tinubu - PDP

A baya kun samu rahoto cewa Jam’iyyar hamayya ta PDP ta fitar da jawabi a ranar Laraba, 8 ga watan Yuni 2022 a game da haduwar da za tayi da Bola Tinubu a 2023.

Mista Debo Ologunagba wanda shi ne sakataren yada labarai na PDP ya fito yana cewa jam’iyyar hamayyar za ta doke Bola Tinubu saboda farin jinin Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Da izinin Allah Kwankwaso ne zai zama shugaban kasa a 2023, in ji Shekarau

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng