2023: Jam'iyyar ADC Ta Sanar Da Wanda Ya Lashe Zaben Fidda Gwaninta Na Shugaban Kasa

2023: Jam'iyyar ADC Ta Sanar Da Wanda Ya Lashe Zaben Fidda Gwaninta Na Shugaban Kasa

  • Mr Dumebi Kachikwu, mai gidan talabijin na Roots ya yi nasarar zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben 2023
  • Kachikwu, wanda kani ne wurin tsohon karamin ministan albarkatun man fetur, Ibe Kachikwu ya doke wasu yan takarar irinsu Kingsley Moghalu a zaben da aka yi a ranar Laraba a Abeokuta.
  • Kachikwu ya yi alkawarin cewa zai yi wa dan takarar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu da na PDP, Alhaji Atiku Abubakar da saura ritaya a 2023

Mai gidan talabijin din Roots Television, Dumebi Kachikwu, ya yi nasarar zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a zaben 2023, Premium Times ta rahoto.

Ya yi nasarar ne bayan kayar da yan takara irinsu Kingsley Moghalu, Chukwuka Monye, da wasy mutane takwas a yayin zaben fidda gwanin shugaban kasa da aka yi a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Tinubu: Dole Mu Tabbatar PDP Ba Ta Sake Jin Kamshin Mulki Ba

2023: Jam'iyyar ADC Ta Sanar Da Wanda Ya Lashe Zaben Fidda Gwaninta Na Shugaban Kasa
2023: Kachikwu ya lallasa Moghalu, ya zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a 2023. Hoto: @channelstv.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mr Kachikwu, kanin tsohon karamin ministan albarkatun man fetur, Ibe Kachikwu, ya yi nasarar ne bayan samun kuri'u 977 ya kada mai biye masa Mr Moghalu, Channels TV ta rahoto.

Mr Moghalu, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, ya zo na biyu da kuri'u 589 yayin da Mr Monye ya zo na uku da kuri'u 339.

Kachikwu ya sha alwashin yi wa Atiku da Tinubu murabus din siyasa a 2023

A jawabin da ya yi wa daligets kafin zaben, Mr Kachiku ya ce nasararsa zai kawo karshen siyasar yan takarar jam'iyyar APC mai mulki da PDP a zaben 2023.

"Na gabatar da kai na ba domin na fi kowa cancanta ba a nan, amma saboda ina kishin kasarmu da inda ta dosa.

Kara karanta wannan

Kiristoci yan arewa 4 da dayansu zai iya zama abokin takarar Tinubu

"Na gabatar da kai na domin Ubangiji ya bani ikon fafatawa da Atiku da Tinubu domin in musu ritaya," ya ce a wurin taron.

Bayan shan kayen da ya yi a ranar Laraba, akwai yiwuwar Mr Moghalu ba zai yi takara a zaben shugaban kasar na 2023 ba.

A matsayinsa na dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar YPP a zaben 2019, Moghalu ya samu kuri'u 21,886 a babban zaben kasa inda ya zo na 14, a zaben da Muhammadu Buhari na APC ya zo na daya.

2023: Tambuwal Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Gwamnonin PDP Suka Yi Taro Da Atiku

A wani rahoton, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2023, Atiku Abubakar, ya yi ganawar sirri da gwamnoni da aka zaba a karkashin jam'iyyar.

Wasu majiyoyi da suke da masaniya kan taron sun shaida wa Vanguard cewa wannan taron shine na farko cikin taruruka da za a yi don shirin kamfen din babban zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164