Shugaban kasa Buhari ya mika tutar takarar shuugaban kasa ga Bola Tinubu

Shugaban kasa Buhari ya mika tutar takarar shuugaban kasa ga Bola Tinubu

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya damƙa tutar APC hannun ɗan takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a Abuja
  • Babban mai taimaka wa shugaban kan harkokin midiya, Buhari Sallau, ya ce hakan ta faru ne gaban kusoshin jam'iyya yayin rufe taro
  • Bola Tinubu ya samu nasarar lashe zaɓen fidda ɗan takara ne bayan lallasa manyan yan takara a wurin taron

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya miƙa turar jam'iyyar APC ga Bola Ahmed Tinubu a wurin babban taro na zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa a Abuja.

Babban mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin kafafen sada zumunta, Buhari Sallau, shi ne ya bayyana wannan cigaban tare da Hotuna a shafinsa na Twitter.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kwankwaso Ya Yi Nasarar Zama Dan Takarar Shugaban Kasar Najeriya Na Jam'iyyar NNPP

Buhari ya miƙa wa Tinubu tutar APC.
Shugaban kasa Buhari ya mika turar takarar shuugaban kasa ga Bola Tinubu Hoto: @Buhari Sallau1
Asali: Twitter

Shugaban tare da shugaban jam'iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, da matar Osinbajo, ya damƙa tutar yayin rufe babban taron APC wanda ya tabbatar da Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban kasa.

Hadimin Buhari ya rubuta cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Shugaban ƙasa Buhari tare da shugaban jam'iyya, Abdullahi Adamu, ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu, da matarsa Sanata Oluremi Tinubu, yayin miƙa tuta ga ɗan takara a wurin rufe taro."

Hotunan miƙa tutar APC ga Tinubu

Shugaba Buhari yayin miƙa tuta ga Tinubu.
Shugaban kasa Buhari ya mika turar takarar shuugaban kasa ga Bola Tinubu Hoto: @Buhari Sallau1
Asali: Twitter

Shugaba Buhari lokacin miƙa tuta ga Tinubu.
Shugaban kasa Buhari ya mika turar takarar shuugaban kasa ga Bola Tinubu Hoto: @Buhari Sallau1
Asali: Twitter

Deleget ɗin APC sun zabi tsohon gwamnan a matsayin wanda zai rike tutar jam'iyya zuwa ga nasara a zaben 2023 da ke tafe.

Tinubu ya samu kuri'u 1,271 hakan ya ba shi nasara kan babban abokin takararsa tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, wanda ya samu kuri'u 316 da kuma mataimakin shugaɓan ƙasa, Yemi Osimbajo, me kuri'a 235.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Gwamna ya dakatar ASUU a jiharsa, ya umarci Malaman jami'o'i su koma aiki ko ya ɗau mataki

Da yake jawabin godiya, Bola Tinubu, ya gode wa shugaba Buhari, shugabannin jam'iyya, gwamnoni, Deleget da sauran waɗan da suka taimaka aka ƙatƙare taron lafiya.

A wani labarin kuma ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar ya taya Bola Tinubu murnar lashe tikitin APC

Ɗan takarar shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya aike da sakon taya murna ga jagoran APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Atiku ya tura sako ne biyo bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na fitar da ɗan takara a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262