Da Dumi-Dumi: Gwamna ya dakatar ASUU a jiharsa, ya umarci Malamai su koma aiki

Da Dumi-Dumi: Gwamna ya dakatar ASUU a jiharsa, ya umarci Malamai su koma aiki

  • Gwamnatin jihar Edo ta dakatar da ayyukan dukkan wasu ƙungiyoyi da suka shafi manyan makarantun gaba da Sakandire mallakin jiha
  • Gwamnatin karkashin gwamna Godwin Obaseki ta ce duk wani ma'aikaci da yaƙi bin umarni zata sallame shi daga aiki
  • Haka nan ta umarci shugabannin makarantun da ke karkashinta su gaggauta biyan duk ma'aikata hakkokin su

Edo - Gwamnatin jihar Edo ƙarƙashin gwamna Godwin Obaseki ta dakatar da ayyukan duk wasu ƙungiyoyi a makarantun da suke mallakin jiha, kamar yadda Punch ta rahoto.

Gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne yayin taron majalisar zartarwa na ranar Laraba, biyo bayan zanga-zangar ɗaliban jami'ar Ambrose Alli da ke Ekopoma.

Ɗaliban sun matsa da zanga-zanga ne kan yajin aikin ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa (ASUU) wanda yaƙi ci ya ƙi cinye wa tsawon watanni.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Malik Ado-Ibrahim ya lashe tikitin takarar a YPP ta su Adamu Garba

Yajim aikin ASUU.
Da Dumi-Dumi: Gwamna ya dakatar ASUU a jiharsa, ya umarci Malamai su koma aiki Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Haka na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin gwamna Godwin Obaseki, Crusoe Osagie, ya raba wa manema labarai jim kaɗan bayan taron.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoto ya nuna cewa Sakataren gwamnatin jihar, Osarodion Ogie, ya ce ƙungiyoyin da dakatarwan ta shafa sun haɗa da ƙungiyar ASUU, kungiyar ma'aikatan jami'a, da ƙungiyar manyan malaman jami'o'i.

Sauran ƙungiyoyin da abun ya shafa sune, ƙungiyar malamai da ƙungiyar ma'aikatan da ba malamai ba na Poly, da sauran ƙungiyoyin da suka shafi makarantun gaba da sakandire.

Mista Onogie ya ce:

"Daga wannan sanarwan, muna umartan dukkan harkokin karatu a makarantu mallakin jiha da Malamai su koma bakin aiki nan take."
"Dalibai na dukkanin manyan makarantun gaba da Sakandire su koma su cigaba da ɗaukar darasi yayin da gwamnati zata kula da matakan tabbatar da an cigaba da karatu yadda ya kamata."

Kara karanta wannan

Najeriya ta Dawo Hayyacinta, Za mu batar da Makasan Jama'a, Tinubu Ya Sha Alwashi

Gwamnati ta umarci a biya kowa albashi

Ya ƙara da cewa, "Shugabannin makarantun da abun ya shafa ana umartan su da su biya Albashin da ma'aikata ke bin su bashi nan take."

"Haka nan ana umartan shugabannin jami'ar Ambrose Alli University su zartar da dokar ba aiki ba biyan albashi, da kuma kora da ɗaukar ma'aikata don maye gurbin duk wanda ya ki bin umarnin komawa aiki."

A wani labarin kuma 'Yan takarar shugaban kasa 7 da suka janye wa Bola Tinubu a filin babban taron APC

Bayan tsayin dare ana kaɗa kuri'u da duk abinda ya biyo baya, kwamitin zaɓe ya sanar da Tinubu a matsayin wanda ya lashe tikitin shugaban kasa.

Wasu yan takara sun sadaukar wa Tinubu da burin su, inda suka janye kuma suka mara masa baya, mun tattaro muku su duka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel