Gwabzawar 2023: Tinubu, Kwankwaso, Atiku da 'yan takara 12 da ke son gaje Buhari
Manyan jam'iyyun siyasar Najeriya sun kammala zabukansu na fidda gwanin dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
APC, PDP, NNPP ADC, LP da dai sauran jam'iyyu duk sun fito da wadanda za su gwabza a zaben na 2023, inda kowace jam'iyya ke ci gaba da shirin karbe kujerar Buhari a zaben.
Kowacce jam'iyya na bayyana kwarin gwiwar karbe kujerar ta Buhari, amma zabi dai ya rage wa 'yan Najeriya su zabi wanda ya kwanta musu kuma suka amince da manufofinsa.
Batun manufofi, 'yan siyasa da dama a jam'iyyu da dama sun sha bayyana tagomashin da suka tanadarwa 'yan Najeriya, inda suke yawan lasa wa 'yan kasar zuma a baki cewa suna hango gobe mai kyau.
Ko ya goben za ta kasance? Batu ne na sheke gobe ko kawo sauyi nagari, sai dai wanda ya shaida zaben na 2023.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A rahoton da muka hada, mun tattaro wasu daga cikin jam'iyyu masu tasiri a Najeriya da suka tsayar da 'yan takara da kuma wadanda suka tsayar, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Jerin jam'iyyu da 'yan takarar shugaban kasa na 2023
- APC - Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
- PDP - Alhaji Atiku Abubakar
- NNPP - Eng. Rabiu Musa Kwankwaso
- LP - Peter Obi
- SDP - Prince Adewole Adebayo
- ADC - Dumebi Kachikwu
- YPP - Prince Malik Ado-Ibrahim
- PRP - Kola Abiola
- AAC - Omoyele Sowore
- AA - Hamza Al-Mustapha
- ADP - Yabaji Sani
- APGA - Peter Umaedi
- BP - Sunday Adenuga
- NRM - Okwudili Nwa-Anyajike
- ZLP - Dan Nwanyawu
Babu daga kafa: Tinubu ya bayyana abin da zai yiwa PDP a zaben 2023
A shirin 2023, jigo a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, rahoton Vanguard.
A yanzu dai Tinubu ne zai gwabza da dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar a babban zaben 2023 mai zuwa.
Tsohon gwamnan na Legas ya ce lokaci ya yi da APC za ta fatattaki jam’iyyar PDP da ya zarga da janyo wa al’ummar kasar koma baya.
A kalamansa na karbar nasarar, Tinubu ya caccaki PDP, inda yace babu abin da jam'iyyar ta jawowa Najeriya illa talauci da rayuwar kunci.
Hakazalika, a kalamansa ya nemi goyon bayan dukkan 'yan jam'iyya da kuma ilahirin 'yan Najeriya domin kawo shugabanci nagari da ciyar da Najeriya gaba a zaben 2023.
Atiku Abubakar ya taya Bola Tinubu murnar lashe tikitin APC
A wani labarin na daban, dan takarar shugaban ƙasa da jam'iyyar PDP ta tsayar, Alhaji Atiku Abubakar, ya taya jagoran APC na ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, murnar samun nasara.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ta ya Tinubu murnan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na dandanlin sada zumunta Tuwita.
Tinubu, ya lashe zaɓen fidda ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC bayan shafe kwanaki ana gudanar da babban taron APC na musamman a Abuja.
Asali: Legit.ng