Mun saduda, Tinubu ya lashe zabe kawai: Kakakin kwamitin kamfen Osinbajo

Mun saduda, Tinubu ya lashe zabe kawai: Kakakin kwamitin kamfen Osinbajo

  • Mai magana da yawun kwamitin kamfen Osinbajo yace sun hakura, ya taya Tinubu murna
  • Akinnola wanda lauya ne ya bayyana cewa ko kadan ba ya nadamar yiwa Osinbajo aikin yakin neman zabe
  • Mutan yankin Yarabawa na tuhumar Osinbajo da wadanda suka mai aiki matsayin mayaudara Tinubu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Kakakin kwamitin kamfen Yemi Osinbajo, Richard Akinnola, ya bayyana cewa sun saduda kuma ya taya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, murnar nasarar zaben fidda gwani.

Akinnola, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook ya bayyana cewa dubi ga yadda lamura ke gudana, Tinubu ne zai lashe zaben.

Ya jaddada cewa ko kadan ba ya nadamar goyon bayan Yemi Osinbajo.

Yace:

"Ina tayaka murna, Asiwaju Tinubu, wanda ake kyautata zaton ya lashe zabe."
"A kowani zabe, wajibi ne mutum daya zai yi nasara. Amma ina alfahari da goyon bayan Farfesa Yemi Osinbajo."

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin APC: Taro ya yi dumi, Osinbajo ya fice daga Eagle Square

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ko kadan ba na nadamar goyon bayansa.

Richard
Mun saduda, Tinubu ya lashe zabe kawai: Kakakin kwamitin kamfen Osinbajo Hoto: Richard Akinnola II
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel