Nwajiuba ya bayyana dalilinsa na rashin zuwa Eagle Sqaure duk da yana takara
- Bayanai sun bayyana kan dalilin da ya hana 'dan takarar shugabancin kasa, Emeka Nwajiuba halartar filin wasa na Eagle Sqauare
- Abike dabiri, daya daga cikin shugabannin taron, ta dinga kiran 'dan takaran da ya garzayo mumbari amma aka ji shiru
- 'Dan uwansa ya bayyana cewa, cin amanar da shugabancin jam'iyyar ya yi wa 'dan uwansa ne ya hana shi halartar taron
FCT, Abuja - Chinedu Nwajiuba, kanin karamin ministan ilimi kuma 'dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar APC, Emeka Nwajiuba, ya yi bayanin dalilin da ya hana yayansa halartar zaben fidda gwani da ake yi a Eagle Square, Abuja.
Kanin Nwajiuba ya ce yayan shi ya ki zuwa filin taron ne saboda shugabancin jam'iyyar APC ya ci amanarsa.
Ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar daren jiya, 7 ga watan Yuni kuma Legit.ng ta gani.
An kira sunan Nwajiuba babu adadi domin ya fito yayi jawabi ga jama'ar da suka halarci gangamin taron fidda gwanin amma shiru ka ke ji.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani sashi na takadar ya ce:
"Abokai da yawa sun dinga kira suna tambayar dalilin da ya hana yayana, Dr Chukwuemeka Nwajiuba fitowa domin jawabi a zaben fidda gwani.
"Abu mai sauki. Fahimta daga farko zuwa lokacin da ya shiga lamarin, kuma ganin kansa a matsayin wadanda suka kafa APC da kuma yarjejeniya kamar yadda aka yi yayin zaben shugaban jam'iyyar a watanni kadan da suka gabata.
"Da wannan fahimtar, ana hararo mika tikitin takarar shugabancin kasa na jam'iyyar ga kudu ko kudu maso gabas.
"Hakan aka dinga saka rai har zuwa karshen tattaunawa. Shi, da baya son ya shiga cikin harkallar daloli da nairori, ya sakankance cewa abinda Najeriya ke bukata a yanzu ba iri daya bane da abinda ta ke bukata a baya lokacin da bata kai haka ba.
Kalubalen mu a matsayin kasa ba za a iya shawo kansa ba da irin kokarin da aka yi wurin kirkiro shi."
Zaben Fidda Gwani: Akwai Babban Hatsari da ke Kunno kai, NWC ga Tinubu da Sauran 'yan takarar Kudu
A wani labari na daban, Shugaban matasan jami'iyyar APC na kasa, Dayo Israel ya ja kunnen 'yan takarar shugaban kasa da shugabannin siyasar kudu a kan rashin hadin kai.
Kamar yadda ya ce, akwai 'yan takarar shugaban kasa na kudu suna tsaka mai wuya a zaben fidda gwanin jam'iyyar da ake yi.
Israel ya bukaci 'yan takarar su girmama darajar gwamnonin arewa wajen mika mulki ga kudu.
Asali: Legit.ng