Zaben fidda gwanin APC: Taro ya yi dumi, Osinbajo ya fice daga Eagle Square
- Rahoto ya bayyana cewa, mataimakin shugaban kasa ya fice daga filin taron zaben fidda gwani, saboda wasu dalilai
- Ya fice ne daidai lokacin da ake kammala kada kuri'u a zaben fidda gwanin da jam'iyyar ta gudanar jiya
- Ya zuwa yanzu dai ba a san dalilin fitansa ba, ba a kuma san ko akwai yiwuwar ya dawo wurin taron ba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Da sanyin safiyar Laraba ne Farfesa Yemi Osinbajo ya bar dandalin Eagles Square inda ake gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa na APC, yayin da lamura ke kara fitowa fili cewa burinsa na ya gaji ubangidansa a matsayin shugaban kasar Najeriya mai yiwuwa ya ci tura.
Ana kyautata zaton Osinbajo ne kusa da tsohon gwamnan Legas Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a cikin ‘yan takara 23 da ke neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a 2023, PM News ta ruwaito.
Tsakanin Tinubu da Osinbajo
Sai dai abubuwan da suka faru a dandalin na Eagles Square sun nuna cewa mai yiwuwa ba zai samu damar nasara kan mutumin da ya fara nuna masa siyasa ba ta hanyar nada shi a matsayin babban lauya kuma kwamishinan shari’a a Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya kuma zabe shi a matsayin mataimakin shugaban kasa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari gabanin nasarar da APC ta samu a 2015.
Rahoto ya ce, an yi wa Osinbajo ihu a matsayin maci amana saboda ya fafata da tsohon ubangidansa kuma mai taimaka masa a lokacin da ya isa dandalin Eagle Square da yammacin jiya Talata.
Al'amura sun kara ta'azzara ga Osinbajo yayin da tsohon maigidan nasa ya samu goyon bayan wasu tsaffin gwamnoni guda biyu, gwamna mai ci, tsohon kakakin majalisa da kuma mafi karancin shekaru a cikin 23 da suka tsaya takara.
Sai dai babu tabbas ko mataimakin shugaban kasar ya bar dandalin Eagles bisa hasashen faduwa a zaben fidda gwanin ko kuma kawai ya wuce ne don shakatawa da yiwuwar ya dawo kafin a fara kirga kuri’u da kuma bayyana sakamakon zaben.
Haka nan wani rahoton jaridar Leadership ke bayyana cewa, akwai yiwuwar Tinubu ya lashe zaben.
An kuma: Gwamnoni sun rage yawan 'yan takarar shugaban kasan APC zuwa uku
A wani labarin, Gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun kara rage jerin sunayen ‘yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar a zaben fidda gwanin shugaban kasa zuwa uku, rahoton Vanguard.
Da sanyin safiyar Talata ne gwamnonin suka gabatar da jerin sunayen mutane biyar ga shugaban kasa Muhammadu Buhari domin a tantance su saboda a cimma matsaya daya.
Wadanda aka fara gabatar da su ga Buhari su ne: ne Asiwaju Bola Ahmed Tinubu; Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Rotimi Amaechi; Gwamna Kayode Fayemi da Gwamna Dave Umahi.
Asali: Legit.ng