Shugaban APC na kasa ya bada sharadin cancanta da zama Magajin Buhari a zaben 2023
- Shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu ya gabatar da jawabinsa a wajen zaben tsaida gwani
- Sanata Adamu ya ce APC na bukatar shugaban da zai iya bunkasa tattalin arziki ya gyara kasa
- Ya wajaba jam’iyyar APC ta hada-kai kafin ta iya samun nasara a zabe mai zuwa inji Adamu
Abuja - Shugaban APC na kasa baki daya, Abdullahi Adamu ya yi magana a game da wanda ya kamata ya karbi mulki a hannun Muhammadu Buhari.
A ranar Laraba, 7 ga watan Yuni 2022 ne Daily Trust ta rahoto Sanata Abdullahi Adamu yana mai bayanin wanda ya fi dacewa da samun takara a APC.
Ku na sane da cewa duk wanda ya yi nasara a zaben da ake gudanarwa shi ne zai yi wa APC takarar kujerar shugaban kasa a farkon shekarar badi.
Abdullahi Adamu ya ce wajibi ne ‘dan takarar APC a zaben shugaban kasa mai zuwa ya zama mutum ne wanda zai iya bunkasa tattalin arzikin kasa.
Da yake yin jawabi a wajen zaben ‘dan takara a farfajiyar Eagle Square da ke garin Abuja, Adamu ya ce APC na bukatar wanda zai iya yin jagoranci na gari.
Tsohon gwamnan na Nasarawa ya kuma bayyana cewa akwai bukatar wanda zai rikewa APC tuta ya yi tarayya da Muhammadu Buhari wajen manufofi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jaridar ta rahoto Sanata Adamu yana jan-kunne da cewa bai kamata wannan zabe ya raba kan ‘ya ‘yan jam’iyyar APC da za su fuskanci babban zabe ba.
Har ila yau, Adamu ya tabbatar da cewa akwai kokarin da ake yi na dinke barakar da za a samu.
A jawabinsa, shugaban na APC na Najeriya ya gargadi ‘ya ‘yan jam’iyya mai mulki da cewa ba za a iya cin ma nasara a zabe, muddin ba a samu hadin-kai ba.
“Babu abin da za mu iya idan ba mu hada-kai ba. Dole ne mu kintsa gidanmu.” - Abdullahi Adamu
Masu nazarin siyasa su na ganin cewa takarar kujerar shugaban kasa a APC zai kasance ne tsakanin Yemi Osinbajo da Bola Tinubu daga kudu maso yamma.
Tinubu na cikin matsala - Fayose
Kamar yadda aka ji labari a jiya, Ayodele Peter Fayose ya rubuta wata budaddiyar wasika zuwa ga Bola Tinubu mai neman takarar kujerar shugaban kasa a APC.
Tsohon gwamnan na jihar Ekiti ya nunawa 'dan takarar cewa rayuwarsa ta na fusakantar barazana kamar yadda ta faru da Obafemi Awolowo da MKO Abiola.
Asali: Legit.ng