Abin da ya jawo kwatsam aka daina zabe wajen fito da wanda zai yi wa APC takaran 2023

Abin da ya jawo kwatsam aka daina zabe wajen fito da wanda zai yi wa APC takaran 2023

  • Dazu aka dakatar da kada kuri’u a wajen zaben wanda zai yi wa jam’iyyar APC takara a 2023
  • An daina zaben ne a lokacin da ‘ya ‘yan jam’iyya na jihar Kano suke kokarin kada kuri’unsu
  • Kwamiti ya dauki wannan mataki saboda gudun a samu rudani wajen tattara sakamakon zabe

Abuja - Labari ya zo mana a ranar Laraba, 8 ga watan Yuni 2022 cewa an dakatar da kada kuri’a a farfajiyar Eagle Square inda APC ta ke tsaida ‘dan takara.

Daily Trust ta rahoto cewa an daina kada kuri’un ne kwatsam yayin da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC na reshen jihar Kano suke kokarin zaben ‘dan takararsu na 2023.

An ga shugaban APC na reshen Kano, Abdullahi Abbas yana faman gardama da wasu jami’ai kafin kwamitin gudanar da zaben ya dauki wannan mataki.

Kara karanta wannan

Peter Obi da Atiku ba su yi barci da wuri ba ba, sun yi magana a kan zaben ‘dan takaran APC

Alhaji Abdullahi Abbas shi ne ya jagoranci ‘ya ‘yan APC daga jihar Kano zuwa wajen zaben.

Wadanda suka kada kuri’arsu daga Kano ba su wuce mutane 20 a lokacin da aka dakatar da zaben. Jihar ta na da ‘yan jam’iyya sama da 120 da za su yi zabe.

Rahoton ya ce an fara kada kuri’u ne da kimanin karfe 2:00 na daren yau. Jami’an tsaro da ma’aikatan da wakilan ‘yan takara duk su na sa ido a filin zaben.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

APC takara a 2023
Zaben 'dan takaran APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Akwai masu neman takaran da ke da fiye da wakili guda a rumfunan zabe, hakan ya jawo hatsaniya. A karshe kwamiti ya bukaci a rage yawan wakilan.

Mutane 9 sun yi waje

Kafin a fara zaben, shugaban kwamitin wannan aiki watau Sanata Atiku Abubakar Bagudu ya bayyana cewa mutum 14 za su gwabza wajen neman tikitin APC.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin APC: Zan amshi sakamakon da zuciya daya – Yerima

Ragowar mutane tara sun janye takararsu don haka ba za a kada masu kuri’a ba kamar yadda Gwamnan na jihar Kebbi ya shaida kafin a fara gudanar da zaben.

Meya sa aka dakatar da zabe?

Dalilin dakatar da zaben na wani ‘dan lokaci shi ne saboda gudun a samu rudani wajen kada kuri’a. Tuni dai abubuwa sun cigaba da tafiya yadda ya kamata.

Akwai ‘yan takara uku da suke dauka da Ahmed a cikin sunansu, a dalilin haka ne kwamiti ya dauki mataki saboda gudun samun matsala wajen tattara sakamako.

Legit.ng Hausa ta fahimci za a iya samun matsala ne wajen sunan Sanata Ahmad Lawan, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da kuma Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura.

'Yan takara sun ragu?

A ranar Talata an ji labari cewa Kabiru Ibrahim Gaya ya ce takarar za ta zama tsakanin mutum biyu ne a zaben tsaida gwani tsakanin Yemi Osinbajo da Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Masu neman kujerar shugaban kasa a APC sun ragu, an bar mutum 2 kacal

Sanatan ya tabbatar da cewa za a samu ‘dan takarar shugaban kasa na 2023 ne daga kudu maso yammacin Najeriya. Amma abin da ke faruwa ya nuna akasin haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng