Zaben fidda gwanin APC: Zan amshi sakamakon da zuciya daya – Yerima

Zaben fidda gwanin APC: Zan amshi sakamakon da zuciya daya – Yerima

  • Daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Ahmad Yerima, ya magantu a kan matakin da zai dauka a karshen zaben
  • Yerima ya bayyana cewa yana fatan lashe tikitin amma zai karbi sakamakon a duk yadda ya zo
  • Ya ce Allah ne ke baiwa dan adam mulki ba mutum ba don haka duk abun da ya nufa shine zai tabbata

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma mai neman takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Ahmad Yerima, ya yi alkawarin karbar sakamakon zaben fidda gwani da zuciya daya.

Yerima ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Eagle Square, filin babban taron jam’iyyar cewa yana fatan samun tikitin jam’iyyar a karshen taron.

Zaben fidda gwanin APC: Zan amshi sakamakon da zuciya daya – Yerima
Zaben fidda gwanin APC: Zan amshi sakamakon da zuciya daya – Yerima Hoto: @LeadershipNGA
Asali: Twitter

Ya ce:

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwani: 'Yan takarar Kudu maso Gabas sun tura wasika ga Buhari kan batun zabo magajinsa

“Ina fatan cewa zan lashe zaben, amma duk abun da ya faru, shine nufin Allah.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Babu wanda zai iya ba mutum mulki sai Allah.
“Don haka, duk abun da ya faru, shine nufin Sa kuma zan karbe shi da hannu bibbiyu.”

Vanguard ta kuma rahoto cewa Yerima ya jinjinawa shugabancin jam’iyyar da ya shirya babban taro na lumana.

“Da izinin Allah, ingantaccen dan takara zai bayyana ga APC, koda ba ni bane.
“Da zaran an kammala zaben, wani zai bayyana. Ana sanya ran dukkanin yan takarar da basu kai labari ba za su karbi lamarin da kyau.”

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC

A gefe guda, Legit Hausa ta kawo cewa jam'iyyar APC na gudanar da zaben fitar da gwani cikin 'yan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Rikici a APC yayin da ake yunkurin magudi a jerin sunayen deliget

Daga cikin 'yan takara, duk wanda ya lashe zaben yau shi ne zai samu tikitin fitowa takarar shugabancin kasa a zaben 2023 mai zuwa a karkashin jam'iyyar mai mulki.

Akwai 'yan takara har 22 da deliget 2322 daga jihohi 36 na kasar nan za su zaba, wanda hakan ne zai bayyana makomar 'yan takarar bayan kammalar zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng