Da Dumi-Dumi: Kotu ta soke wani zaɓen fidda gwanin jam'iyyar APC

Da Dumi-Dumi: Kotu ta soke wani zaɓen fidda gwanin jam'iyyar APC

Abuja - Babbar Kotun tarayya dake zamanta a Abakalike, ta soke zaben fidda gwanin PDP na ɗan takarar gwamnan jihar Ebonyi wanda aka sake shirya wa.

Punch ta rahoto cewa Kotun ta yanke cewa zaɓen fitar da ɗan takara wanda ya gudana a ranakun 5 da 6 ga watan Yuni, 2022 ya saɓa wa doka kuma ta soke shi.

Kotun ta ƙara da cewa sabon zaɓen wanda ya ayyana Sanata Obinna Ogba a matsayin wanda ya lashe tikiti ya saba wa kundin mulkin Najeriya.

Amma Kotun ta tabbatar da zaɓen farko wanda ya gudana a ranar 29 ga watan Mayu, 2022, wanda ya ayyana Dakta Ifeanyi Odii a matsayin wanda ya lashe tikitin takarar gwamana a PDP.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel