Yanzun nan: Shugaba Buhari ya amince da wasu yan takara da gwamnoni suka miƙa masa ya zaɓa

Yanzun nan: Shugaba Buhari ya amince da wasu yan takara da gwamnoni suka miƙa masa ya zaɓa

  • Gwamnan Filato, Simon Lalong, ya ce shugaban ƙasa Buhari ya aminta da dukkan yan takara 5 da muka kai masa gabanin fara zaɓe
  • Gwamnan wanda ke jagorantar gwamnonin arewa ya ce ba zai yuwu su tafi wurin zabe da dukkanin yan takara ba
  • A cewarsa, Buhari ya ce kowane ɗaya daga cikin su ya cancanta ya gaje shi, kuma ya ba APC gudummuwa matuƙa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan Filato, Simon Lalong, ya bayyana martanin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, bayan miƙa masa sunayen yan takara biyar.

Gwamna Lalong ya faɗi matsayar da shugaban kasa ya gaya musu ne yayin zantawa da kafar Talabijin ta Channels tv, ranar Talata.

Yan takara guda biyar.
Yanzun nan: Shugaba Buhari ya amince da wasu yan takara da gwamnoni suka miƙa masa ya zaɓa Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Lalong ya ce kowane ɗaya daga cikin yan takaran guda biyar sun cancanta kuma suna da kwarewar zama shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Sanatan APC: Yan takara uku sun janye wa mataimakin shugaban ƙasa Osinbajo

A kalamansa ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Shugaban ƙasa ya gaya mana cewa kowane ɗaya daga cikin yan takara biyar ɗin nan sun cancanta su zama shugaban ƙasa kuma sun ba da gudummuwa matuƙa ga APC. Ya ce zuciyarsa ta natsu da kowane ɗayan su."
"Mun yanke wannan shawarin ne domin samun haske yayin da zamu tafi zuwa zaben fidda gwani. Ba zamu tafi da kowa ba amma a tunanin mu, waɗan nan ya kamata mu tafi da su."
"Kwamitin tantance yan takara ya gabatar da rahoto bayan kammala aikinsa kuma ya ba kowane ɗan takara makin da ya ci, duk da cewa babu wanda aka soke."

Suwaye waɗan nan yan takara?

Punch ta rahoto cewa gwamnonin arewa sun miƙa wa Buhari sunayen wasu yan takara 5 gabansa gabanin fara fafatawa a zaben fidda gwani.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Babbar Kotu ta soke zaɓen fidda ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP

Yan takarar da sunan su a bayyana a cikin jerin sun haɗa da, Bola Tinubu, Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi, gwamna Kayode Fayemi da kuma gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi.

A wani labarin na daban kuma Bayan zaftare yan takara zuwa biyu, An matsawa Osinbajo ya janye don tabbatar da magajin Buhari

Yankin kudu maso yammacin Najeriya na kokarin ganin an kawo karshen rikicin neman tikitin takarar shugaban kasa a APC.

Wasu bayanai sun nuna cewa yan takara sun zama biyu, kuma Sarakuna sun matsawa Osinbajo lamba ya janye wa Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262