2023: Shugaban PDP Ya Bayyana Abin Da Yasa Za Su Ci Zaben Shugaban Kasa Da Jihohi Da Dama a Najeriya

2023: Shugaban PDP Ya Bayyana Abin Da Yasa Za Su Ci Zaben Shugaban Kasa Da Jihohi Da Dama a Najeriya

  • Sanata Iyorchia Ayu, shugaban jam'iyyar PDP na kasa ya ce jam'iyyarsa ce za ta lashe zaben shugaban kasa da mafi yawan jihohi a 2023
  • Ayu ya yi wannan furucin ne a ranar Talata a hedkwatar PDP a Abuja yayin zantawa da manema labarai bayan mika takardun cin zabe ga yan takarar gwamna na PDP
  • Ayu ya ce yan Najeriya ba su gamsu da irin kamun ludayin gwamnatin APC ba karkashin Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnonin jihohi don haka yana kyautata zaton za su zabi PDP

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya ce yana kyautata zaton cewa jam'iyyarsa za ta ci zaben shugaban kasa da mafi yawancin jihohin kasar a 2023, rahoton Vanguard.

Ayu ya bayyana hakan ne yayin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai bayan mika takardun shaidan cin zabe na wadanda suka yi nasara a zaben fidda gwani na gwamnoni a Abuja, ranar Talata.

Kara karanta wannan

Za ku taro rikici: Yahaya Bello ya fadi abu daya da zai hana shi takara a zaben fidda gwanin APC

2023: Shugaban PDP Ya Bayyana Abin Da Yasa Za Su Ci Zaben Shugaban Kasa Da Jihohi Da Dama a Najeriya
2023: Abin da yasa PDP za ta kwato karin wasu jihohi daga hannun APC, Ayu. Hoto: @VanguardNGR.
Asali: UGC

APC ta gaza inganta tattalin arziki, tsaro da sauran abubuwa, Ayu

Ya ce dalilinsa shine mafi yawancin yan Najeriya sun gaji da rashin iya shugabanci musamman bangaren tattalin arziki da tsaro da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnonin APC suka yi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ayu ya ce:

"PDP ce za ta yi nasara a 2023, ba kawai jihohin da muke rike da su za mu ci ba, za mu kwato wasu karin jihohin domin gwamnonin mu sun tabbuka abin azo a gani kuma yan Najeriya ba su ji dadin kamun ludayin gwamnati mai ci yanzu ba."

Kaduna: Jam'iyyar NNPP Mai Kayan Marmari Ta Zabi Tsohon Sanata A Matsayin Dan Takarar Gwamna

A wani rahoton, Sanata Suleiman Hunkuyi, a jiya ya zama dan takarar gwamna na jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) bayan samun kuri'un daligets guda 732, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

An kuma: Gwamnoni sun rage yawan 'yan takarar shugaban kasan APC zuwa uku

Dan takarar na NNPP zai fafata da Mohammed Ashiru na jam'iyyar PDP da Uba Sani na jam'iyyar APC da wasu yan takarar gwamnan daga wasu jam'iyyu a zaben na 2023.

Hunkuyi ya wakilci mazabar Kaduna North a majalisar dattawa a majalisa zubi ta 8 karkasin APC kafin ya koma PDP a 2019.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164