Da duminsa: EFCC suna "aikin sirri" a filin zaben fidda gwani na APC, Majiya ta tabbatar
- Majiya mai karfi daga hukumar EFCC ta ce jami'anta suna filin zaben fidda gwanin jam'iyyar APC a Abuja inda suke aikin sirri
- A cewar majiyar, suna lura tare da kiyaye kan siyan kuri'u, karbar cin hanci da rashawa tare da sauran abubuwan damfara da ka iya faruwa
- Zuwan jam'an EFCC ba ya rasa alaka da labaran siyan deliget da manyan 'yan takara ke yi kan kudi $40,000
FCT, Abuja - Wata majiya mai karfi a Hukumar Yaki da Rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta tabbatar da cewa jami'an hukumar na aikin sirri wurin lura da deliget tare da kiyaye yadda ake siyan kuri'u a zaben fidda gwani na jam'iyyar APC mai mulki.
Majiyar abin dogaro, wacce ta yi magana da Punch kan a boye sunanta, ta ce, "A halin yanzu muna filin zaben fidda gwani a sirrance. Muna lura kuma muna kallon yadda ake cusawa deliget ra'ayi, ake siyan kuri'u da sauran magudin zabe na kudi da ka iya faruwa."
Majiyar ta tabbatar da cewa, hukumar EFCC na aikin sirrin domin kama mahandama ta hanyar yi musu ba-zata.
Wannan rahoton na zuwa ne bayan batun da ke yawo na cusawa deliget $40,000 wanda manyan 'yan takara ke badawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwana goma cif da ta gabata kenan da jami'an hukumar EFCC suka dira filin wasa na Mashood Kashimawo Abiola da ke Abuja yayin da ake gudanar da zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP.
Jami'an sun dira wurin karfe 4 na yamma.
An gano cewa, jami'an sun dira filin zaben ne bayan rahoton siyan kuri'u da cin hanci da ake bai wa deliget ya watsu.
A yayin da aka nemi jin ta bakin mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya ki yin tsokaci a kan hakan.
EFCC ta bayyana dalilinta na yin dirar mikiya a filin zaben fidda gwanin PDP na kasa
A wani labari na daban, Hukumar yaki da almundahana tare hana yi wa tattalin arzirkin kasa zagon kasa (EFCC), ta bayyana yadda jami'anta suka yi dirar mikiya wajen da ake gudanar da zaben fidda 'dan takarar shugaban kasa na babbar jam'iyyar adawa.
Ana taron ne a Moshood Kashimawo Abiola National Stadium a Abuja. Jami'an sun bayyana ne don sa ido a kan yadda ake shakara wa wakilan jam'iyya kudi da tare da almubazzaranci.
Asali: Legit.ng