Gwamnonin APC sun gabatarwa Buhari jerin sunayen yan takarar shugaban kasa 5

Gwamnonin APC sun gabatarwa Buhari jerin sunayen yan takarar shugaban kasa 5

  • Gwamnoni karkashin inuwar jam'iyyar APC sun gabatarwa shugaban kasa Muhammadu Buhari sunayen wasu masu neman takarar tikitin shugaban kasa na jam'iyyar guda biyar
  • Ana sanya ran shugaban kasar zai zabi dan takarar maslaha a cikin yan takarar da aka gabatar masa wadanda dukkaninsu yan kudu ne
  • Yan takarar wadanda aka gabatar masa a safiyar yau Talata sune Bola Tinubu, Yemi Osinbajo, Dave Umahi, Rotimi Amaechi da kuma Kayode Fayemi

Abuja - Gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun gabatar da sunayen yan takarar shugaban kasa guda biyar a gaban shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya zabi dan takarar maslaha daga cikinsu, Daily Trust ta rahoto.

Wata majiya abun dogaro ta bayyana cewa gwamnonin sun gabatar da sunayen ne a safiyar Talata, 7 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Ba zai taba goyon bayan Tinubu ba: Sule Lamido ya bayyana mutum 2 da Buhari yake so ya tsayar a 2023

Gwamnonin APC sun gabatarwa Buhari jerin sunayen yan takarar shugaban kasa 5
Gwamnonin APC sun gabatarwa Buhari jerin sunayen yan takarar shugaban kasa 5 Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Kamar yadda Sahara Reporters ta rahoto daga majiya, sunayen mutane biyar da aka gabatarwa shugaban kasar sune:

  1. Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo
  2. Tsohon gwamnan jihar Lagas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
  3. Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi
  4. Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi
  5. Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan ganawarsu da shugaban kasa, gwamnonin sun bayyana cewa za su koma fadar shugaban kasa bayan sun zauna da kwamitin aiki na jam’iyyar ta kasa, NWC da sauran masu ruwa da tsaki.

Majiyar ta ce:

“Sun zabi mutum daya daga kudu maso gabas, daya daga kudu maso kudu sannan uku daga kudu maso yamma daidai da matsayinsu na cewa ya kamata a mika mulki ga yankin kudu."

Ya ce ana sanya ran shugaban kasar zai zabi mutum daya daga cikin wadannan jerin sunaye.

Za a gudanar da zaben fidda gwanin jam’iyyar a yau Talata. Shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan a matsayin dan takarar maslaha. Sai dai an nuna adawa da hakan.

Kara karanta wannan

2023: El-Rufai, Zulum da sauran gwamnonin arewa masu goyon bayan kudu maciya amana ne – Kungiyar arewa

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC

Agefe guda jam'iyyar APC na gudanar da zaben fitar da gwani cikin 'yan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar.

Daga cikin 'yan takara, duk wanda ya lashe zaben yau shi ne zai samu tikitin fitowa takarar shugabancin kasa a zaben 2023 mai zuwa a karkashin jam'iyyar mai mulki.

Akwai 'yan takara har 22 da deliget 2322 daga jihohi 36 na kasar nan za su zaba, wanda hakan ne zai bayyana makomar 'yan takarar bayan kammalar zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng