Da dumi-dumi: Bani da wani takamamman zababben dan takara, inji shugaba Buhari

Da dumi-dumi: Bani da wani takamamman zababben dan takara, inji shugaba Buhari

  • Batu ya fito fili, shugaban kasa ya ce babu wanda ke ransa da zai zaba a matsayin dan takarar da zai gaje shi a 2023
  • Ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala tattaunawa da gwamnonin APC na yankin Arewacin Najeriya
  • Duk dai wannan na zuwa ne daidai lokacin da APC ke gudanar da zabukan fidda gwaninta na shugaban kasa gabanin 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin din nan ya bayyana cewa ba shi da wani wanda ya zaba ya gaje shi a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da za a yi ranar 7 ga watan Yuni, 2022.

Shugaban ya kuma ce ya amince da matsayin gwamnonin APC na Arewa cewa a mayar da mulki zuwa yankin kudancin kasar nan a 2023, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya magantu kan hanyar da za a bi wajen zabar dan takarar APC

Hakan dai na faruwa ne yayin da gwamnonin APC na Arewa suka yi watsi da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello saboda adawa da matsayarsu na cewa mulki ya koma kudu.

Bani da zababben dan takara, inji Buhari
Da dumi-dumi: Babu wanda na ware a matsayi magaji, inji shugaba Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawar sirri da shugaba Buhari shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya bayyana cewa shugaban kasar ya bayyana karara cewa ba shi da wani zababben dan takarar shugaban kasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

“Daga cikin waccan tattaunawar, shugaban kasa, a matsayinsa na mai imani da tsarin dimokuradiyya, ya yi imanin cewa kowane dan takara dole ne ya fito ta hanyar gaskiya.
“Shugaban kasar ya shaida mana cewa a wannan zaben, a yanzu, ba shi da wani zababben dan takara, don haka ya umurci kungiyar gwamnonin APC su gana da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa domin su amince tare da samar da mafita da shawarwari don maye gurbinsa.”

Kara karanta wannan

Zaben Ahmad Lawan zai barka Gwamnonin APC, sun ce dole mulki ya koma Kudu a 2023

Ya ce shugaba Buhari ya umurci kungiyar gwamnonin da su gana da kwamitin NWC don karin shawarwari kan tsarin da aka amince da shi wajen zaben dan takarar jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023, Channels Tv ta ruwaito.

Daga karshe: Dan takarar shugaban kasa a APC ya janye saboda wasu dalilai

A wani labarin, Ken Nnamani, tsohon shugaban majalisar dattawa, ya fice daga takarar neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, TheCable ta ruwaito.

Tsohon dan majalisar ya bayyana janyewarsa ne a wata ganawa da ya yi da manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Ya ce:

“A halin da ake ciki yanzu, ba wani ma’ana in ci gaba da takara domin ban samu damar tallata bayanai na da ra’ayoyina ga wakilan jam’iyyarmu ba ta hanyar da za ta ba da damar shawarwari da fahimtar juna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.