Jajiberin Zaben Fidda Gwani: Buhari Ya Ci Abincin Dare Tare da Adamu da Gwamnoni
- Sa'o'i kadan kafin zaben fidda gwani na 'yan takarar shugabancin kasa na APC, Buhari ya karba bakuncin wasu jiga-jigan jam'iyyar
- Sanata Abdullahi Adamu, Bisi Akande, John Oyegu, Sanata Iyiola Omisore tare da wasu gwamnonin APC sun ci abincin dare tare da Buhari
- An gano cewa, hakan yana daga cikin tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da ya ke yi domin fitar da 'dan takarar da ya dace
FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a daren Lahadi, ya karba bakuncin wasu daga cikin mambobin jam'iyyar APC na kasa inda suka ci abincin dare a dakin taro na Banquet da ke fadarsa a Abuja.
Shugabancin APC da suka halarci liyafar cin abincin daren sun hada da shugaban jam'iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, tsohon shugabannin ta, Bisi Akande, John Oyegu, sakataren jam'iyyar, Sanata Iyiola Omisore da wasu gwamnonin APC.
Taron yana daga cikin cigaba da tuntube-tuntube da shugaban kasar ke yi da masu ruwa da tsani kan zaben yardajjen 'dan takarar shugaban kasan a jam'iyyar kafin zaben fidda gwanin da za a yi gobe Litinin, Punch ta ruwaito..
A wani taron da shugaban kasan yayi da 'yan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC a daren Asabar, Buhari ya bukaci 'yan takarar da su zabi tsayayyen 'dan takara daya daga cikinsu kuma zai cigaba da tattaunawa da masu ruwa da tsani na jam'iyyar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce "Wannan ne karo na biyi a jere kuma zan cigaba da ganawa da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar. Ana daukan wadannan matakan ne domin tabbatar da hadin kan jam'iyyar ya cigaba kuma a samar da alkibla."
Hotuna: Shugaba Buhari ya shiga ganawa da yan takarar kujerar shugaban kasa karkashin APC
A wani labari na daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin masu takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Al Progressives Congress APC da yammacin Asabar, 4 ga Yuni, 2022.
Buhari ya gayyace liyafar abincin dare ne fadar shugaban kasa dake Aso Villa, Abuja. Kimanin mutum 20 ke hallare a zaman.
Wadanda ke hallare a liyafar sun hada da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Farfesa Yemi Osinbajo, Dave Umahi, Ibikunle Amosun, Kayode Fayemi da Shugaban APC Abdullahi Adamu.
Asali: Legit.ng