Hotuna: Shugaba Buhari ya shiga ganawa da yan takarar kujerar shugaban kasa karkashin APC

Hotuna: Shugaba Buhari ya shiga ganawa da yan takarar kujerar shugaban kasa karkashin APC

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin masu takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Al Progressives Congress APC da yammacin Asabar, 4 ga Yuni, 2022.

Buhari ya gayyace liyafar abincin dare ne fadar shugaban kasa dake Aso Villa, Abuja.

Kimanin mutum 20 ke hallare a zaman.

Wadanda ke hallare a liyafar sun hada da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Farfesa Yemi Osinbajo, Dave Umahi, Ibikunle Amosun, Kayode Fayemi da Shugaban APC Abdullahi Adamu.

Hakazalika akwai Ogbonnaya Onu, Emeka Nwajuiba, Ken Nnamani, Tein Jack-Rich, Yahata Bello, Mohammed Badaru Abubakar.

Hotuna
Hotuna: Shugaba Buhari ya shiga ganawa da yan takarar kujerar shugaban kasa karkashin APC Hoto: @BuhariSallau1
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asali: Legit.ng

Online view pixel