2023: Tinubu, Osinbajo da Sauran 'yan Takarar APC na Kudu Maso Yamma Sun Sanya Labule

2023: Tinubu, Osinbajo da Sauran 'yan Takarar APC na Kudu Maso Yamma Sun Sanya Labule

  • Yayin da ake ta shirye-shiryen ganin an fidda 'dan takarar shugaban kasa a jam'iyya mai mulki ta APC na 2023, 'yan takarar shugaban kasa na kudu maso yamma da wasu masu rike da mukaman jam'iyyar sun gana da juna a Abuja
  • Wata majiya ta bayyana yadda taron ya gabata daga daren Asabar zuwa safiyar Lahadi, inda suka tattauna a kan yadda zasu fidda 'dan takarar da zai kare martabar jam'iyyarsu
  • Taron yazo ne bayan wasu awanni da gwamnonin arewa na APC 11 suka bukaci a bada tiketin tsayawa takarar shugaban kasa ga kudu, tare da umartar duk wasu 'yan takara daga arewa da su janye

FCT, Abuja - Duba da yadda zaben fidda gwani na APC ke karatowa, 'yan takarar shugaban kasa daga kudu maso yamma da masu rike da mukaman jam'iyya mai mulki ta APC suka gana a Abuja.

Kara karanta wannan

Zaben Fidda Gwani: Matasan Kano Sun Balle Zanga-Zanga kan Hukuncin Gwamnonin APC

Wata majiya wacce ta bukaci a sakaya sunanta ta tabbatar da ganawar ga Channels TV ta waya a ranar Lahadi.

2023: Tinubu, Osinbajo da Sauran 'yan Takarar APC na Kudu Maso Yamma Sun Sanya Labule
2023: Tinubu, Osinbajo da Sauran 'yan Takarar APC na Kudu Maso Yamma Sun Sanya Labule. Hoto daga Duoye Diri
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, ganawar ta gabata ne a daren Asabar zuwa safiyar Lahadi.

Duk da ba a samu cikakken bayani game da ganawar ba har zuwa lokacin da aka tattara wannan rahoton, an tattaro yadda yadda 'yan takarar suka tattauna a kan yadda yankin za su zabi 'dan takarar da zai kare martabar jam'iyyar.

Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo; jagoran APC, Bola Tinubu; Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti; tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun.

Wasu daga ciki sun hada da babban mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ajayi Borroffice; Tsohon kakakin majalisar dattawa, Dimeji Bankole; da faston jihar Legas, Tunde Bakare.

Kara karanta wannan

Manyan matsaloli 4 da ke gaban APC yayin da zaben fidda gwani ya gabato

Saura sun hada da gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas, Dapo Abiodun na Ogun, Gboyega Oyetola na Osun da Rotimi Akeredolu na Ondo.

An gabatar da taron ne bayan wasu awanni da gwamnonin APC na arewa suka bukaci jam'iyyar ta bada tikitin takarar shugabancin kasa na jam'iyyar ga kudu.

A wata takarda da gwamoni 11 suka rattaba hannu, sun yi hakan ne don girmama jam'iyyar APC.

Gwamnonin sun bukaci dukkan 'yan takarar arewa da su janye bukatar takarar shugabancin kasa.

"Wannan lokaci ne na tsanani da bada gudunmawa wajen zaben 'dan takarar jam'iyyar mu," a cewar gwamnonin.

Babu 'dan takarar da APC ta yi watsi da shi yayin tantancewa, Mamban Kwamitin Tantancewa

A wani labari na daban, wani mamban kwamitin tantancewa na jam'iyyar APC ya yi karin haske dangane da batun jam'iyyar na dakatar da wasu 'yan takarar shugaban kasa cikin mutane 23 da suka bayyana gabanta.

Kara karanta wannan

2023: Muhimman dalilai 3 da za su iya sa Tinubu ya rasa tikitin takarar shugaban kasa a APC

Ya bayyana wa Premium Times a daren Juma'a cewa, ba daidai ba ne rahoton da aka dinga yadawa dangane da cewa kwamitin ta dakatar da 'yan takara 13.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng