Ni na ba ka mulki: Tinubu ya caccaki gwamna ido-da-ido kan goyon bayan Osinbajo

Ni na ba ka mulki: Tinubu ya caccaki gwamna ido-da-ido kan goyon bayan Osinbajo

  • Gwamnan jihar Ogun ya sha caccaka daga bakin jigon jam'iyyar APC Tinubu kan batun tsayawa takara
  • Tinubu ya bayyana cewa, shi ya daura gwamnan a matsayin gwamna a zaben 2023, don haka dole ya saka masa
  • Ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga deliget-deliget na APC a jihar gabanin zaben fidda gwani

Ogun - Jaridar Punch ta ruwaito cewa, na gaba-gaba a tseren tikitin takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bol Tinubu ya yi ikrarin cewa ya daura gwamna Dapo Abionun na Ogun a shekara ta 2019.

Ya yi magana ne a masaukin shugabab kasa na Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, yayin jawabi ga deliget-deliet na APC kafin zaben fidda gwanin shugaban kasa na APC.

Tinubu na tare da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da takwaransa na jihar Kano, Umar Ganduje da kuma tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a lokacin.

Tinubu ya caccaki gwamna, ya ce shi ya daura shi mulki
Ni na ba ka mulki: Tinubu ya caccaki gwamna ido-da-ido kan goyon bayan Osinbajo | Hoto: an24.net
Asali: UGC

Gwamna Abiodun a baya ya fito fili ya amince da aniyar takarar Osinbajo. Osinbajo dai ya fito ne daga Ikenne da ke karamar hukumar Ikenne a jihar Ogun, rahoton Daily Trust.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da alamu Tinubu bai gamsu da amincewar da Abiodun ya yi wa Osinbajo ba.

Da yake magana a Abeokuta ranar Alhamis, Tinubu, wanda ya yi magana da harshen Yarbanci, ya caccaki gwamnan.

Ya ce:
“Sama da shekara 25 ke nan ina yi musu hidima. Wannan wanda ke zaune a baya na, Dapo, zai iya cewa zai iya zama Gwamna ba tare da ni ba?
"Muna tare a filin wasa na MKO Abiola, yana da masaniya, ba sa son a ba shi tutar jam’iyya, ni ne na mika masa tutar. Ya san ba zai iya zama gwamna ba sai da taimakon Allah da goyon bayana.

"Idan yana son haduwa da Allah a daidai wurin da ya dace, lallai ne ya san cewa in ba dan ni da Allah ba, da bai zama Gwamna ba."

Tinubu ya kuma bayyana yadda ya jagoranci gwagwarmayar da ta kai ga hambarar da gwamnatin PDP a zaben 2015.

A jawabinsa, Abiodun wanda a baya ya bayyana goyon bayansa ga takarar Osinbajo, ya ki amincewa da aniyar Tinubu.

Ya gaya wa Tinubu cewa deliget-deliget daga jihar za su yi "abin da ya dace" a zaben fidda gwani.

Abiodun ya bayyana Tinubu a matsayin jarumin siyasa, wanda ke cin nasara kuma mai dabaru.

Dan takarar shugaban kasa ya tono sirri: Ba dan ni ba da Buhari ya sha kaye a zaben 2015

A wani labarin, daya daga cikin jiga-jigan ‘yan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya jagoranci gwagwarmayar siyasar da ta kai ga hayewar shugaban kasa Muhammadu Buhari mulki a 2015.

Tinubu ya kuma ce shi ya kawo Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin abokin takarar Buhari, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi magana ne a dakin taro namasaukin shugaban kasa da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, yayin da yake jawabi ga deliget din jam’iyyar APC gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel