2023: Muhimman dalilai 3 da za su iya sa Tinubu ya rasa tikitin takarar shugaban kasa a APC

2023: Muhimman dalilai 3 da za su iya sa Tinubu ya rasa tikitin takarar shugaban kasa a APC

Jagoran jam'iyyar APC ta kasa, Asiwaju Ahmed Tinubu, bai yi kasa a guiwa ba wajen bakado dukkan sirri, yayin fafutukar ganin ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2023.

A watan Fabrairu, Tinubu ya fara fafutukar bayan daukar tsawon shekaru yana tsara yadda zai dare madafun iko.

2023: Muhimman dalilai 3 da za su iya sa Tinubu ya rasa tikitin takarar shugaban kasa a APC
2023: Muhimman dalilai 3 da za su iya sa Tinubu ya rasa tikitin takarar shugaban kasa a APC. Hoto daga @OfficialABAT
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan Legas din ya dira fadar shugaban kasa a Aso Rick don bayyana muradinsa na takarar shugaban kasa, wanda ya siffanta da abun da ya dade yana buri.

Kafin zaben fidda gwanin jam'iyyar APC da ke karatowa, baya ga Tinubu akwai wasu 'yan takara 22 dake fafutukar ganin sun samu tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

Hotuna: 'Yan a mutun Jonathan sun mamaye hedkwatar APC suna neman a ba shi tikiti

Saboda irin yadda ya dauki tsawon shekaru yana tsari gami da shirin tare da tara magoya baya a Najeriya wanda hakan ba abu bane mai sauki, tare da sadaukarwa, nuna halin dattako, ba gudu ba ja da baya, gami da mayar da hankalinsa gaba daya, ba zai yi wa Tinubu wahalar lallasa sauran abokan takararsa a gasar ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai, akwai wasu sabbin matakai da cigaba da za su iya dakile Tinubu daga samun damar amsar tikitin duk da tsawon shekarun da ya dauka yana shiri.

Rashin samun goyon bayan Buhari

A siyasar Najeriya, shugaban kasa ba mulkin kasa kadai yake ba, shi ne shugaban jam'iyya mai mulki.

Hakan na nuna cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari na da mahimmiyar rawa da zai taka wajen zabar wanda za a bawa tikitin tsayawa takarar shugaban sannan kuma magajinsa a 2023.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ina zama shugaban kasa zan saki shugaban IPOB Nnamdi Kanu, dan takara

Akwai rade-radin cewa shugaban kasa Buhari baya son abokin siyasarsa, Bola Tinubu ya gaje shi a 2023.

Abun takaici, an samu labarin yadda shugaban kasar baya da ra'ayin Tinubu ya gaje shi, duk da Tinubu ya taka mahimmiyar rawa wajen ganin shugaban kasar ya lallasa abokin takararsa, Goodluck Jonathan a shekarar 2015, bayan ya sha kaye sau uku.

Yayin da magoya bayan tsohon gwamnan Legas din suka yi imani da cewa duk da haka zai iya nasarar lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar APC ba tare da Buhari ya mara masa baya ba, shugaban kasar ya ba su mamaki a ranar Talata, 31 ga watan Mayu yayin da ya sanar da cewa zai zabi wanda zai gaje shi bayan an yi sulhu da sauran masu neman tikitin.

Da alamun da Buhari ke nunawa, ba zai dauki Tinubu a matsayin wanda zai gajeshi ba.

Kamar yadda Daily Trust ta bayyana, wani ministan Buhari ya ce Buhari bai gamsu da Tinubu ya zama magajinsa a shekarar 2023 ba.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa ya tono sirri: Ba dan ni ba da Buhari ya sha kaye a zaben 2015

Wani ministan a shugaban kasa wanda ba a ambaci sunansa ba ya kara da cewa, Buhari bai boye matsayarsa ba na rashin amincewa a takarar Tinubu.

"Shugaban kasa bai yi amanna da takarar Tinubu ba saboda bai gamsu da cewa Asiwaju shi ne 'dan takarar da ya cancanci ya gaje shi ba," a cewar ministan.
"Mun yi imani da cewa Tinubu ba zai kare wa Buhari martabarsa ba bayan ya sauka daga madafun iko, saboda haka akwai bukatar a sake duba wani bangaren.
"Muna iya kokarin ganin mun gamsar da shugaban kasa da ya marawa 'dan takarar da zai kare masa martawa baya bayan saukarsa daga madafun iko," an yanko maganar majiyar.

Haka zalika, Ade Bash, wani mai tsokaci a kan siyasa, ta bayyanawa Legit.ng yadda alamu ke nuna yadda Tinubu zai yi nasarar lashe zaben fidda gwanin idan APC ta yi amfani da zaben kai tsaye ko wanda ba na kai tsaye ba a zaben fidda gwanin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Shugabanci a 2023: Obasanjo na bakin ciki da yadda Atiku ya samu tikitin takara a PDP, yana shirya masa tuggu

Dalilin da yasa gwamnonin APC da wakilan zabe zasu bi bayan Buhari karkashin jagorancin Babatunde Obele

"Ko da APC ta yi amfani da matakin kai tsaye, akwai yuwuwar Tinubu ya ci. Idan ma APC batayi amfani da matakin kai tsaye ba, shima akwai yuwuwar Tinubu ya lashe zaben," a cewarsa.

Sai dai, masu kiyasin siyasa sun ce babu tabbacin Tinubu zai yi nasara idan APC ta zabi tsarin sulhu wajen zaben 'dan takarar shugaban kasarta.

Baraka da aka samu a tushen siyasar Tinubu

Har yanzu, tsarin siyasar Tinubu tana da matukar karfi. Sai dai, ya rasa wasu magoya baya masu matukar amfani da suke hada da ministan cikin gida, Rauf Argebesola.

Hakazalika, akwai 'yan siyasa masu yawa da suka hada da Osinbajo da Gwamna kayode na jhar Ekiti, wadanda za su goyi bayan Tinubu, amma sai kwatsam suka fito takara.

Tsoron kafuwa tare da samun karfin iko

A watan Maris da Tinubu ya gana da 'yan majalisar wakilai na APC domin neman goyon bayansu, ga abinda shugaban masu rinjaye, Ado Doguwa yace:

"Gida ka ke saboda kana tare da 'ya'yanka maza da mata da za ka bugi kirji ka ce naka ne, wadanda suka mora daga kokarin da ka yi a rayuwarsu da siyasarsu a kasar nan."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng