2023: Abin Da Bashir El-Rufai Ya Yi Alƙawarin Aikatawa Idan Peter Obi Ya Ci Zaɓe Ya Tada Ƙura a Twitter

2023: Abin Da Bashir El-Rufai Ya Yi Alƙawarin Aikatawa Idan Peter Obi Ya Ci Zaɓe Ya Tada Ƙura a Twitter

  • Bashir El-Rufai, dan Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya yi alkawarin zai hau duwatsun Zuma da Aso Rock a ya rubuta 'Bashir Akuya Ne' idan Peter Obi ya ci zaben 2023
  • Peter Obi, a baya-bayan nan ya fice daga jam'iyyar PDP ya koma Labour Party inda ya samu tikitin takarar zaben shugaban kasa a 2023
  • Matasa da dama musamman daga kudancin Najeriya a dandalin sada zumunta suna matukar nuna goyon bayansu ga Peter Obi suna mai cewa sun gaji da APC da PDP

Bashir El-Rufai, dan gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya bayyana abin da zai aikata idan dan takarar shugaban kasa na Labour Party Peter Obi ya lashe zaben 2023 da ke tafe.

Bashir, a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a ya ce zai hau Dutsen Zuma a Jihar Niger da Dutsen Aso Rock a Abuja, ya rubuta baro-baro cewa "Bashir El-Rufai akuya ne".

Kara karanta wannan

Watakila magana ta canza, Gwamnonin APC su na ta haduwa da Osinbajo a Aso Villa

2023: Abin Da Bashir El-Rufai Ya Yi Alƙawarin Aikatawa Idan Peter Obi Ya Ci Zaɓe Ya Tada Ƙura a Twitter
Bashir El-Rufai: Abin da zan aikata idan Peter Obi Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa. @Mobile_Punch.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Idan Peter Obi ya zama shugaban kasar Najeriya, na yi alkawarin zan hau Dutsen Zuma daAso Rock da fenti in rubuta 'Bashir El-Rufai akuya ne," in ji shi.
"Zan rubuta a shahararren fuskar dutsen ta yadda kowa zai iya gani, kuma zan yi amfani da samfurin rubutu da launi da ko cikin dare ne za a iya ganinsa, ko adana wannan rubutun."

2023: Abin Da Bashir El-Rufai Ya Yi Alƙawarin Aikatawa Idan Peter Obi Ya Ci Zaɓe Ya Tada Ƙura a Twitter
Bashir El-Rufai ya ce zai hau duwatsu ya yi rubutu a cewa shi 'akuya' ne idan Peter Obi ya ci zabe. Hoto: @BashirElRufai.
Asali: Twitter

A wani rubutu da ya wallafa tunda farko a Twitter, Bashir ya yi ikirarin cewa ya san dan takarar da Shugaba Muhammadu Buhari ke son ya gaje shi a jam'iyyar APC amma ba zai iya bayyana sunayensu ba don sirri ne.

Martanin wani ma'abota amfani da Twitter kan rubutun.

@CJMOOREPLUG ya ce:

"Ko da baka fada a fili ba, kowa na iya gani ta yadda mutumin ke murmushi a talabijin. APC da PDP duk yan barkwanci ne. Tun 1998, babu wani abu da ya canja a Najeriya. Zaben 2023 zai fita daban. Ko dai Peter Obi ko kuma kowa ya kama gabansa. Ba za mu iya cigaba haka ba."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci Ana Kwana Kadan Zaben Fidda Gwani Na Yan Takarar Shugaban Kasa a APC

Wasu yan Najeriya da dama suma sun nuna rashin jin dadinsu da wannan kalaman na Bashir suna mai cewa su matasa za su tabbatar Peter Obi ya yi nasara.

Peter Obi, ya fice daga jam'iyyar PDP ya koma Labour Party inda ya samu tikitin takarar zaben shugaban kasa a 2023.

Katsina Ba Ta Siyarwa Ba Ce, Ɗalibai Ga Wakilan Jam'iyyu

A wani rahoton, Kungiyar Hadin Kan Daliban Jihar Katsina ta shirya zanga-zangar lumana musamman ga wakilan manyan jam’iyyu akan su zabi ‘yan takarar gwamna na kwarai wadanda za su ciyar da jihar gaba.

Daily Trust ta ruwaito cewa daliban sun dinga zagaye manyan titinan da ke garin Katsina rike da takardu wadanda su ka rubuta, “Jihar Katsina ba ta siyarwa ba ce”.

Yayin zantawa da manema labarai, shugaban daliban, Aliyu Mamman, ya nemi wakilan su duba zabin da ke zuciyoyin mutanen jihar wadanda su ka zarce mutane miliyan takwas a zuciyarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164