Shugaba Buhari zai gana da yan takarar shugaban ƙasa, zai faɗi sunan wanda yake so ya gaje shi a 2023
- Wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta fallasa wasu shirye-shiryen Buhari gabanin zaɓen fidda gwanin APC
- Bayanan sun ce Buhari zai gana da dukkanin yan takarar jam'iyyar APC kuma zai bayyana wanda yake goyon bayan ya gaje shi
- Haka nan da yuwuwar shugaban zai tafi Ghana yau Asabar amma zai dawo gida duk a yau kuma ya gana da yan takara
Abuja - Ana tsammanin Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai gana da yan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC nan da ranar Lahadi mai zuwa, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Wasu bayanai sun nuna cewa shugaban ƙasan na shirin tafiya zuwa ƙasar Ghana yau Asabar ba tare da warware batun maslaha da ya jawo rikici a jam'iyya mai mulki ba.
Wani babban jami'in gwamnati ya shaida wa ɗaya daga cikin wakilan jaridar da sharaɗin ɓoye bayanansa cewa shugaba Buhari zai dawo gida idan ya tafi Ghana duk a yau Asabar.
Buhari, wanda bai jima da dawowa daga ƙasar Spaniya ba, da yuwuwar ya sa labule da yan takarar shugaban ƙasan da daren Asabar ko kuma ranar Lahadi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majiyar ta ce:
"Muna tsammanin shugaban ƙasa zai tafi Ghana gobe (Yau Asabar) bayan nan ana ganin zai gana da yan takara wanda yayin haka zai bayyana wanda yake son ya gaje shi, wanda yake goyon bayan APC ta ba tikiti."
Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa shugaban ƙasa Buhari ya gana da baki ɗaya gwamnonin cigaba na APC ranar Talata da ta gabata gabanin taron zaɓen fidda gwani.
Taron ya zo a lokacin da ake yaɗa jita-jitar cewa da yuwuwar shugaban ƙasa ya zaɓi ɗan takarar da yake son jam'iyyar ta goya wa baya a zaɓen 2023.
Buhari ya kuma roki gwamnonin su tabbatar da babban taron da ke gabatowa na zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa bai saɓa wa abubuwan da aka kafa APC domin su ba.
A wani labarin kuma Magajin Buhari a 2023: An bayyana sunayen yan takarar APC 5 da zasu iya lallasa Atiku cikin sauki
Honorabul Farouk Aliyu ya ce akwai yan takarar shugaban ƙasa sama da 5 a APC da zasu iya lallasa Atiku cikin sauki a 2023.
Jigon jam'iyyar APC mai mulki ya ce Atiku ba kanwar lasa bane da zasu saki jiki, zasu yi aiki tukuru don tabbatar da nasara.
Asali: Legit.ng