Tashin hankali: Gwamnonin APC za su yaki ‘Dan takarar da Buhari zai fito da shi a 2023

Tashin hankali: Gwamnonin APC za su yaki ‘Dan takarar da Buhari zai fito da shi a 2023

  • Wasu Gwamnoni ba su amince Muhammadu Buhari ya zauna shi kadai ya fito da ‘dan takara ba
  • Gwamnoni na APC da suke kan wa’adi na biyu su na son samun ta-cewa a kan zabin shugaban kasa
  • Akwai masu kawo shawarar jam’iyya ta sake bude saida fam domin wasu ‘yan takarar su shiga lissafi

Abuja - Abubuwa ba su tafiya daidai a jam’iyyar APC kan maganar zabin da shugaba Muhammadu Buhari yake son yi na ‘dan takarar shugaban Najeriya.

Leadership a rahoton da ta fitar ranar Juma’a ta ce wasu gwamnoni sun nuna ba su amince shugaban kasa ya rike wuka da nama a kan batun magajinsa ba.

Rahoton da mu ka samu shi ne gwamnonin APC sun raba kansu gida-gida, inda kowanensu yake yin taro domin ganin ya samu nasara wajen fito da ‘dan takara.

Kara karanta wannan

Takarar Tinubu, Osinbajo, Amaechi da Lawan a 2023 ta na raba kawunan na-kusa da Buhari

A ranar Alhamis, wata majiya ta shaidawa jaridar cewa gwamnonin jihohin sun gagara zama a karkashin jagorancin kungiyarsu ta PGF a kan wannan batun.

Gwamnonin su na cigaba da yin shawara ne a kan wanda ya kamata jam’iyya mai mulki ta ba takarar shugaban kasa, domin ya gaji Muhammadu Buhari.

Majiyar tace ana sa rai daga baya kan gwamnonin ya hadu, duk da ‘yan sabanin da suke samu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnonin APC
Gwamnonin APC a fadar Shugaban kasa Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Zaben gwani ko ayi maslaha?

Haka zalika gwamnonin ba su tare da shugaban kasa a maganar fito da ‘dan takara ta hanyar maslaha, su na ganin ya kamata a shirya zaben tsaida gwani.

Abin ya kai wasunsu su na jin haushin yadda aka bar kofar takara a bude ga tsiararrun 'yan takara daga yankunan Arewa maso gabas da Arewa ta tsakiya.

A sake bude saida fam?

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa 9 su na goyon APC ta tsaida ‘dan Kudu ya zama Shugaban kasa a 2023

Jaridar ta ce kungiyar gwamnonin na PGF ta na ganin ya kamata a kara bude saida fam din shiga takara, domin a samu ‘yan siyasa da za su shiga neman kujerar.

Amma gwamnonin kudu sun raba jiha a kan wannan, su na ganin an rufe saida fam din takara.

Gwamnonin da suke kammala wa’adinsu a shekarar nan ko shekara mai zuwa, su ne ba su goyon bayan shugaban kasa ya zauna shi kadai, ya fito da ‘dan takara.

Shugaban Najeriyan ya na kasar Sifen yanzu haka, amma zai dawo kafin ranar zaben fitar da gwani. A lokacin ake sa ran zai yi zama da duk gwamnonin APC.

Mulki ya koma Kudu - Gwamnoni

Ana da labari a cikin gwamnonin akwai masu ra’ayin cewa daga yankin Arewacin Najeriya ya kamata a samu wanda zai karbi mulki a hannun Buhari a 2023.

Amma akwai Gwamnonin Arewa tara da su na goyon APC ta tsaida ‘dan Kudu ya zama Shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng