Na hango nasara ne, shiyasa na rabu da Saraki, na bi layin Atiku a PDP inji Dino Melaye
- Ana zargin Dino Melaye da cewa ya juyawa Bukola Saraki baya a 2023, ya bi layin Atiku Abubakar
- Melaye bai goyi bayan tsohon shugaban majalisar dattawa a zaben fitar da gwanin jam’iyyar PDP ba
- Tsohon Sanatan ya ce dalilin yin hakan shi ne Atiku zai samu gwaggwabar nasara a zabe mai zuwa
Abuja - Tsohon Sanatan Kogi ta yamma a majalisar dattawa, Dino Melaye ya bayyana cewa yana goyon bayan Atiku Abubakar ne domin shi zai ci zabe.
Da aka zanta da shi a wani shiri a gidan talabijin na TVC, Sanata Dino Melaye ya yi ikirarin Atiku Abubakar zai samu gagarumar nasara a zabe na 2023.
‘Dan siyasar yana sa ran ‘dan takarar shugaban kasar na PDP zai ba sauran jam’iyyu tazara mai yawa a zaben sabon shugaban kasa na shekarar badi.
A cewar fitaccen ‘dan majalisar, an yi adalci da gaskiya a zaben fitar da ‘dan takaran shugaban kasa da jam’iyyar PDP ta gudanar a makon da ya wuce.
Ya aka yi Dino ya bar Saraki?
Melaye ya amsa tambaya a game da dalilinsa na goyon bayan Atiku Abubakar a PDP, bayan kuwa da farko an san cewa yana cikin yaran Bukola Saraki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanatan ya bayyana cewa bai canza gida ba, kuma a lokacin da yake goyon bayan tsohon shugaban majalisar dattawa, ya yi masa biyayya 100%.
“Ban canza sheka daga goyon bayan Saraki zuwa Atiku ba. Na kasance ina goyon bayan Saraki 100% a lokacin da na ke tare da shi.”
“Ba ni da wata matsala da Saraki, ko a yau da safe na hadu da shi, mu ka sha dariyanmu.”
Ana bukatar mai hada kan mutane
“Wannan karo na zabi Atiku ne domin dole in yi tarayya da wanda kowa ya san shi. A yanzu ana bukatar wanda zai hada-kan Najeriya.”
“Ba a bukatar wanda ake yi wa kallon Musulmi ko Kirista. Atiku mutum ne da ya shahara, wanda babu inda sunansa bai shiga a kasa ba."
“Don na tashi daga wajen wanda ba a san da shi ba, zuwa wajen wanda aka sani, ban canza gida ba, na bi wanda zai iya gyara Najeriya ne.”
- Dino Melaye
Punch ta rahoto Melaye yana cewa jam’iyyarsa ta PDP za ta iya karbe mulki daga hannun APC domin Atiku yana da lafiya da basira, kuma ya kware a siyasa.
Yamutsi a gidan APC
Ku na da labari cewa Gwamnoni biyar sun saye fam din takarar shugaban kasa, amma da alama dukkansu ba za su kai labari a zaben fitar da gwanin APC ba.
Manyan masu neman takaran su na neman daurin gindi da kamun kafa a wajen wadanda suka shaku da Muhammadu Buhari domin su samu tikitin APC.
Asali: Legit.ng