Takarar Tinubu, Osinbajo, Amaechi da Lawan a 2023 ta na raba kawunan na-kusa da Buhari
- A halin yanzu an shiga rudani, Gwamnoni na kai-komo domin ‘dan takaransu ya kai labari a APC
- Gwamnoni biyar suke neman kujerar shugaban kasan APC a 2023, amma kusan ba a maganarsu
- Wadanda ke gaba-gaba a takara su ne: Bola Tinubu, Rotimi Amaechi, Yemi Osinbajo da Ahmad Lawan
Abuja - Jagororin jam’iyyar APC sun samu kansu a wani yanayi a game da zabin wanda zai zama ‘dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023.
Daily Trust ta ce wannan ya sa masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC suke ta lissafi domin tunkarar zaben fitar da gwani da za a soma daga ranar Litinin.
Gwamnoni 5 su na takara
Akwai gwamnoni biyar da suke neman kujerar shugaban kasa a APC; Yahaya Bello, Dr. Kayode Fayemi, David Umahi, Ben Ayade da Badaru Abubakar.
Jaridar ta fahimci cewa mafi yawan gwamnoni su na neman a fito da ‘dan takarar shugaban kasa ne daga wajen abokan aikinsu, wasu ‘yan siyasan dabam.
Ana ta zama iri-iri domin ganin an cin ma matsaya a kan wanda APC za ta ba tikitinta a zaben 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Masu kamun kafa sun dage
Masu neman takara su na ta lallaban Hadimai da ‘yanuwan shugaban kasa domin su samu fada, a kuma tallata takararsu a wajen mai girma shugaban kasa.
Majiya ta shaidawa jaridar cewa Buhari yana shawara ne da wasu tsirarrun mutane na kusa da shi wanda Malam Mamman Daura yake jagorantar aikinsu.
An cire Jonathan a lissafi
Wannan kamun kafa ya na ta raban kan ‘yan fadar shugaban kasa. Da farko akwai masu goyon bayan Rotimi Amaechi, akwai mutanen Goodluck Jonathan.
A yanzu Dr. Goodluck Jonathan bai cikin lissafin takarar shugaban kasa a 2023, don haka tsohon Ministan sufuri watau Amaechi ya samu dama da kyau.
Irinsu Tukur Buratai suka dage wajen tallata Amaechi wanda ya jagoranci yakin zaben Buhari a 2015 da 2019, kuma yana da kusanci da irinsu Sabiu Abdullahi.
Tinubu ya kafu a APC
Akalla mutane biyu da ke kusa da shugaban kasa ne suke son Bola Ahmed Tinubu. Jaridar ta ce akwai Malam Adamu Adamu da babban hadimi, Yau Darazo.
Haka zalika akwai wasu gwamnoni na APC da-dama da suke tare da Tinubu a zabe mai zuwa.
A gefe guda akwai masu goyon bayan Yemi Osinbajo ya karbi mulki. Sannan wasu sun dauko Ahmad Lawan da ra’ayin ‘Dan Arewa ne kawai zai iya doke PDP.
A makon nan shugaba Muhammadu Buhari ya zauna da gwamnoni, ya kuma nuna masu cewa yana son goyon bayansu wajen zakulo wanda zai gaje shi a badi.
Asali: Legit.ng