2023: Lokaci Na Ne Na Zama Shugaban Kasar Najeriya, In Ji Bola Tinubu

2023: Lokaci Na Ne Na Zama Shugaban Kasar Najeriya, In Ji Bola Tinubu

  • Asiwaju Bola Tinubu, jagoran jam'iyyar APC na kasa ya ce yanzu lokacinsa ne na zama shugaban kasar Najeriya wato a 2023
  • Tinubu ya ce ya shafe fiye da shekaru 25 yana yi wa jam'iyyar APC da yan siyasa da dama hidima don haka lokacin saka masa ya zo
  • Jagoran na jam'iyyar APC ya yi wannan jawabin ne a Jihar Ogun inda ya tafi ganawa da daliget gabannin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam'iyyar APC

Ogun - Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Sanata Bola Tinubu, a ranar Alhamis ya ce shine ya cancanci ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari saboda idan aka yi la'akari da abubuwan da ya yi a baya.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai Abeokuta domin neman goyon bayan daligets gabanin zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa na APC, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

'PDP Ta Kashe Naira Miliyan 12 Don Gina Bandaki 3 Daga Kudin Da Ta Samu Yayin Sayar Da Fom'

Bola Tinubu: Lokaci Na Ne Na Zama Shugaban Kasar Najeriya
Tinubu: Lokaci Na Ne Na Zama Shugaban Kasar Najeriya. Hoto: @VanguardNGR.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jagoran na APC wanda ya yi magana cikin harshen yarbanci, ya tunatar da su irin rawar da ya taka wurin gina jam'iyyar APC har ta zama jam'iyya mai mulki a kasar.

"Ina nan tun lokacin jam'iyyar AD, har ACN wacce daga bisani ta zama APC.
"Na shafe fiye da shekaru 25 kuma na tallafawa mutane da dama sun cimma burinsu na siyasa.
"Gwamnan ku, Dapo Abiodun, ya zama gwamna ne saboda taimakon Allah da taimako na.
"Ku tafi ku duba bidiyon, ba su so bashi tutar jam'iyyar APC ba a zaben gwamna na shekarar 2019 a Ogun.
"Ni ne na dage sai an bashi.
"Idan ba domin ni da na karfafawa Buhari gwiwa kada ya karaya ba, da bai zama shugaban kasa ba," in ji shi.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Dakatar Yakin Neman Zabe Kan Abu Ɗaya Da Ya Shafi Yan Najeriya

"Tunda ya zama shugaban kasa, ban taba neman minista ba ko rokonsa kwangila ko bashi.
"Kawai abin da na ke cewa shine lokacin yarbawa ne su zama shugaban kasa yanzu kuma a cikin yarbawan, lokaci na ne.
"Na raini yara na siyasa da dama, amma a lokaci mai hatsari, dole mutum ya kare kansa da farko.
"Na hidimta ya isa haka, bana son in zama tarihi. Lokaci na ne in zama shugaban kasa. Na cancani wannan abin.
"Mu je zuwa," in ji shi.

Tinubu ya shawarci daligets din su yi watsi da kabilanci yayin zaben fidda gwani na shugaban kasa na APC da ke tafe.

Osinbajo Yana Ganawar Sirri Da Shugaban APC Da Gwamnoni 5 a Ofishinsa

A bangare guda, Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a halin yanzu yana ganawa da a akalla gwamnonin jam'iyyar APC guda biyar da Sanata Abdullahi Adamu shugaban jam'iyyar APC na ƙasa a ofishinsa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wasu Sabbin Hotuna Daga Aso Villa Sun Nuna Tinubu Na Kus-Kus da Mataimakin Buhari

Taron na zuwa ne kwanaki biyu bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin a dakin taro na Council Chambers a gidan gwamnati a ranar Talata kafin ya tafi Madrid, Spain.

Hakan kuma na zuwa ne bayan kammala tantance yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC da kwamitin John Odigie-Oyegun ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164