Babbar magana: Ina zama shugaban kasa zan saki shugaban IPOB Nnamdi Kanu, dan takara

Babbar magana: Ina zama shugaban kasa zan saki shugaban IPOB Nnamdi Kanu, dan takara

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APGA ya bayyana manufarsa ta duba lamarin Nnamdi Kanu
  • Dan takarar wanda gogaggen ma'aikacin shari'a ne ya bayyana cewa, zai saki Nnamdi Kanu saboda wasu dalilai
  • Ya bayyana cewa, zai yi amfani da siyasa wajen tabbatar da sakin Kanu ba atre da samun wata matsala ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APGA Farfesa Peter Umeadi ya ce zai yi la’akari a siyasance ga shugaban 'yan IPOB Nnamdi Kanu ya yafe masa idan ya zama shugaban Najeriya.

Kanu, wanda ke hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) tun shekarar da ta gabata, ana tuhumarsa da laifin cin amanar kasa.

Kuma tsohon Alkalin Alkalan na Jihar Anambra ya yi imanin cewa ta hanyar siyasa, wacce ya kwatanta da afuwa, za ta iya magance matsalar.

Kara karanta wannan

Ni masoyin Arewa ne, zan lallasa Atiku a 2023, 'yan Adamawa ni za su zaba, inji Okorocha

Sakin Nnamdi Kanu: Dan takara ya gano mafita ga matsalar 'yan IPOB
Babbar magana: Ina zama shugaban kasa zan saki shugaban IPOB Nnamdi Kanu, dan takara | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A kalamansa yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Zan yi la'akari da mafita a siyasance. Idan aka yi la’akari ta hanyar siyasa, ba kawai ku sake shi ba.”
“Dole ne ku sanya komai a wurinsa, bayan haka, muna da batun yin afuwa kuma kun san nawa Najeriya ta kashe wajen yin afuwa. Wannan shine mafita ta siyasa. Za mu yi wani abu makamancin haka."

Umeadi, wanda aka zaba a ranar Laraba a matsayin dan takarar APGA, kuma ya yi watsi da maganganun da ke cewa jam'iyyar APGA ba ta da tsari mai karfi na karbar kasar nan.

Ya bayar da hujjar cewa APGA na da shugabanni a fadin kasar nan ciki har da babban birnin tarayya.

A hirar da Channels Tv, ya kawo batutuwa masu yawa kan lamarin da ya shafi Nnamdi Kanu da mambobin kungiyarsa, IPOB.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen 'yan takara 5 da ake sa ran Buhari zai zabi daya don ya gaje shi

Dan takarar shugaban kasa ya tono sirri: Ba dan ni ba da Buhari ya sha kaye a zaben 2015

A wani labarin, daya daga cikin jiga-jigan ‘yan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya jagoranci gwagwarmayar siyasar da ta kai ga hayewar shugaban kasa Muhammadu Buhari mulki a 2015.

Tinubu ya kuma ce shi ya kawo Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin abokin takarar Buhari, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi magana ne a dakin taro namasaukin shugaban kasa da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, yayin da yake jawabi ga deliget din jam’iyyar APC gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.