2023: Ku ba ɗan kudu tikitin takarar shugaban ƙasa idan kuna son cigaba da mulki, Akeredolu ga APC

2023: Ku ba ɗan kudu tikitin takarar shugaban ƙasa idan kuna son cigaba da mulki, Akeredolu ga APC

  • Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu, ya shawarci APC ta tsayar da ɗan kudu ya gaji Buhari idan tana son cigaba da mulki a 2023
  • Gwamnan, wanda aka ba shugaban kwamitin tsaro da haɗa kai na taron fidda gwani, ya ce sun cimma matsaya da sauran gwamnonin kudu
  • Tun bayan bayyana Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar PDP, jam'iyya mai mulki ta kasa zaune ta kasa tsaye kan wanda zai fafata da shi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ce ya kamata jam'iyyar APC ta tsayar ɗan yankin kudu a takarar shugaban ƙasa idan ta na son cigaba da mulki a 2023.

Babban taro na musammann na APC wanda Deleget za su zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa zai gudana ne a ranakun 6,7 da 8 ga watan Yuni, 2022.

Kara karanta wannan

2023: Na fi kowa tsammanin lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a APC, Gwamnan Arewa

Jam'iyyar APC mai mulki ta ayyana sunan gwamnan Ondo a matsayin shugaban kwamitin tsaro da samun haɗin kai a wurin zaben fidda gwanin.

Buhari. gwamna Fayemi da Rotimi Akeredolu.
2023: Ku ba ɗan kudu tikitin takarar shugaban ƙasa idan kuna son cigaba da mulki, Akeredolu ga APC Hoto: Rotimi Akeredolu Aketi/facebook
Asali: Facebook

A wani rubutu da gwamnan ya saki a shafinsa na dandalin Facebook, Gwamna Akeredolu ya ce shi da yan uwansa gwamnoni na kudancin Najeriya karƙashin ƙungiyarsu sun cimma matsaya ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa baki ɗaya mambobin ƙungiyar gwamnonin kudu sun amince cewa ya zama wajibi mulkin ƙasa ya koma hannun ɗan yankin su.

A kalamansa ya ce:

"Wajibi APC ta yi duk me yuwu wa don cigaba da mulki, wajibi mu aiwatar da tsarin karɓa-karɓa matukar muna son cin nasara mu cigaba da mulki. Shikenan."

APC ta shiga ruɗani tun bayan tsaida Atiku

An yi ta yaɗa jita-jitar cewa mai yuwuwa APC ta ba ɗan arewa tikitin takara biyo bayan sakamakon zaben fidda gwanin PDP, wanda ya baiwa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, nasara.

Kara karanta wannan

2023: Ka goya mun baya da zaran ka shiga Abuja, Tinubu ya roki wani wani ɗan takarar shugaban kasa

Wasu bayanai sun nuna cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, na gaba-gaba cikin waɗan da ka iya samun tikitin APC.

Atiku Abubakar da Ahmad Lawan duk sun fito ne daga yanki ɗaya, wato arewa maso gabashin Najeriya.

A wani labarin kuma Magajin Buhari a 2023: An bayyana sunayen yan takarar APC 5 da zasu iya lallasa Atiku cikin sauki

Honorabul Farouk Aliyu ya ce akwai yan takarar shugaban ƙasa sama da 5 a APC da zasu iya lallasa Atiku cikin sauki a 2023.

Jigon jam'iyyar APC mai mulki ya ce Atiku ba kanwar lasa bane da zasu saki jiki, zasu yi aiki tukuru don tabbatar da nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262