2023: Ina da yaƙinin zan lashe tikitin takarar shugaban kasa na APC, Inji Badaru
- Gwamna Muhammed Badaru Abubakar na Jigawa ya ce fatansa na lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na APC ya girma sosai
- Gwamnan, wanda ke fatan gaje shugaba Buhari a 2023, ya ce ba tare da baiwa Deleget kuɗi ba zasu zaɓe shi saboda wasu dalilai
- Badaru ya bayyana cewa dan karan kansa yake neman shugabancin ƙasa, babu wanda ya ba shi umarnin haka
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin ƙasar nan, Muhammed Badaru, ya ce yana fatan ya lashe zaɓen fidda gwanin APC na takarar shugaban ƙasa.
Daily Trust ta rahoto cewa jam'iyyar APC mai mulki ta tsara gudanar da zaɓen fitar da ɗan takararta na shugaban kasa a ranakun 6,7 da 8 ga watan Yuni, 2022.
Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da kafar watsa labarai ta BBC Hausa ranar Litinin 30 ga watan Mayu, 2022.
Badaru ya bayyana cewa tarihin nasarorinsa kaɗai sun isa gamsar da Deleget su kaɗa masa kuri'u ba tare da ya ba su cin hanci ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ƙara da cewa ya ci nasara a ayyuka daban-daban da jam'iyya ta ɗora masa, inda ya ce ya jagoranci APC ta samu nasara a wani a zaɓe a jihar Bayelsa.
Yayin da aka tambayeshi ko yana ganin zai lallasa sauran yan takara a zaɓen fid da gwanin APC, Badaru ya ce:
"Fatan da nake ya girma, na ziyarci sassan ƙasar nan kan aikin jam'iyyar APC kuma na kammala su da nasara. Na ci nasarar wani zaɓe a jihar Bayelsa, na je Ondo, Ogun, Osun da Bauchi, da wasu wurare don aikin Kamfe."
"Duk waɗan nan ayyukan na yi nasara akan su. Don haka Deleget sun mun kyakkyawan sani kuma nima na san su. Na jagoranci babban taron APC, sun ga irin ayyukana, ni na jagoranci kwamitin zaɓe a taron mu na bayan nan."
"Mun yi alaƙa mai kyau da su (Deleget). Na je wurare da dama a sassan ƙasar nan domin lalubo hanyar sulhu ko harkokin zaɓe ko tantance yan takara. Suna ganin girma na, Deleget zasu iya karɓan kudi hannun yan takara kuma su zaɓi nagari."
Shin Buhari ne ya umarci ka shiga tseren takara?
Sai dai, gwamnan ya ce shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, be umarce shi da ya nemi tikitin takarar shugaban kasa a 2023 ba.
Legit.ng Hausa ta tuntuɓi wani mai bibiyar harkokin siyasa mazaunin Birnin Kudu a jihar Jigawa, Aminu Aminu, ya shaida mana cewa suna yi wa gwamnan su fatan Alherri.
Aminu, wanda mamba ne na jam'iyyar APC ya koka kan irin mutanen da gwamna Badaru ya goyi baya APC ta tsayar da Jigawa.
A kalamansa ya shaida wa wakilin mu cewa:
"Muna wa Badaru fatan Alkairi a siyasarsa ta gaba amma shugabancin ƙasar nan ba abu ne mai sauki ba, samun tikitin APC cikin waɗan nan yan takara gaskiya zai yi wahala ga Badaru."
"Sai dai a nan Jigawa muna ganin ya kama hanyar rusa APC baki ɗaya. Wanda ya tsaida mana a gwamna ba son shi muke ba, yanzu fa manyan ƴaƴan jam'iyya ka iya fita ko kuma su ci dinduniyar jam'iyya."
A wani labarin na daban kuma Gwamnan PDP ya canza mataimaki yayin neman tazarce a 2023
Saɓanin da ya shiga tsakanin gwamnan Oyo, Seyi Makinde, da mataimakinsa ya jawo gwamnan ya fasa neman tazarce tare da shi a 2023.
Gwamnan ya bayyana ɗaukar sabon wanda zai zama mataimakinsa, Bayo Lawal, yayin da zai nemi tazarce a zaben 2023.
Asali: Legit.ng