Da dumi-dumi: Gwamnan PDP ya canza mataimaki yayin neman tazarce a 2023

Da dumi-dumi: Gwamnan PDP ya canza mataimaki yayin neman tazarce a 2023

  • Saɓanin da ya shiga tsakanin gwamnan Oyo, Seyi Makinde, da mataimakinsa ya jawo gwamnan ya fasa neman tazarce tare da shi a 2023
  • Gwamnan ya bayyana ɗaukar sabon wanda zai zama mataimakinsa, Bayo Lawal, yayin da zai nemi tazarce a zaben 2023
  • Mataimakin gwamna na yanzun, Injiniya Olaniyan, ya yi zargin cewa Uban Gidansa ba ya tafiya da shi a harkokin gwamnati

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Oyo - Yayin da ake ta shirye-shiryen tunkarar 2023, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya aje mataimakinsa na yanzu, injiniya Rauf Olaniyan, a matsayin wanda zai nemi tazarce tare da shi.

Maimakon haka, gwamnan ya zaɓi shugaban hukumar gidaje ta jihar Oyo, Bayo Lawal, a matsayin sabon wanda zai taimaka masa a zaɓen gwamnoni na 2023.

Leadership ta ruwaito cewa Makinde ya zaɓi Lawal ya zama mataimakinsa ne a gaban wasu mutum biyu, waɗan da aka yada jita-jitar mai yuwuwa ɗayan su ya maye gurbin Olaniyan.

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.
Da dumi-dumi: Gwamnan PDP ya canza mataimaki yayin neman tazarce a 2023 Hoto: Seyi Makinde/facebook
Asali: Facebook

Lawal, wanda ya fito daga yankin ƙaramar hukumar Irepo na jihar Oyo, ya rike kujerar Antoni Janar na jihar kuma an naɗa shi a shekarar 1999 karkashin mulkin tsohon gwamna Lam Adesina.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka nan kuma, Gwamna Seyi Makinde a zangon mulkinsa na yanzu, ya sake naɗa shi shugaban hukumar gidaje ta jihar Oyo, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Meyasa gwamnan ya ɗauki wannan matakin?

Gwamna Makinde da mataimakinsa Injiniya Olaniyan ba su ɗasa wa a yan kwanakin nan da suka gabata.

Injiniya Olaniyan, wanda ya yi zargin gwamna ya maida shi saniyar ware, ya ce bai tsoma kansa cikin zaɓukan fitar da yan takara a kujeru ɗaban-daban da ya gudana a jihar ba.

Mataimakin gwamnan ya ƙara da cewa raɗe-raɗin zai sauya sheka zuwa wata jam'iyya ya yaɗu kamar wutar daji saboda ya yi gum da bakinsa bai tanka ba.

Da yake tsokaci kan zaɓukan fidda gwani da suka zakulo yan takarar da jam'iyyar PDP ta tsayar a babban zaɓen 2023 da ke tafe, Olaniyan ya ce:

"Bai kamata ku tsaya kuna hasashe ba saboda a ranar Sallah na faɗa wa mutane gaskiyar abin da ke cikin zuciyata."

A wani labarin kuma Magajin Buhari a 2023: An bayyana sunayen yan takarar APC 5 da zasu iya lallasa Atiku cikin sauki

Honorabul Farouk Aliyu ya ce akwai yan takarar shugaban ƙasa sama da 5 a APC da zasu iya lallasa Atiku cikin sauki a 2023.

Jigon jam'iyyar APC mai mulki ya ce Atiku ba kanwar lasa bane da zasu saki jiki, zasu yi aiki tukuru don tabbatar da nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel