2023: Har yanzu Atiku Abubakar bai zaɓi wanda zai zama mataimaki ba, Hadimi

2023: Har yanzu Atiku Abubakar bai zaɓi wanda zai zama mataimaki ba, Hadimi

  • Mai magana yawun Alhaji Atiku Abubakar, Mista Paul Ibe, ya ce har yanzun Uban Gidansa bai zaɓi wanda zai zama mataimakinsa ba
  • Ya ce raɗe-raɗin da ake yaɗa wa a kafafen sada zumunta na zaɓan wani tsohon gwamna a Imo ba gaskiya bane
  • Ya nemi yan Najeriya su yi hakuri idan lokaci ya yi za'a fitar da sanarwa a hukumance ba sai sun yaɗa ƙanzon kurege ba

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 da ke tafe na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, bai zaɓi wanda zai zama mataimakinsa ba har yanzun, a cewar hadiminsa, Mista Paul Ibe.

Mista Ibe ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa raɗe-raɗin da ke yawo a bakunan mutane da kafafen sada zumunta cewa Atiku ya zabi tsohon gwamnan Imo, Emeka Ihedioha, ba gaskiya bane.

Kara karanta wannan

Tinubu ya saki sabon Bidiyo, ya faɗi inda zai nufa idan ya sha ƙasa a zaɓen fidda gwanin APC

Atiku Abubakar.
2023: Har yanzu Atiku Abubakar bai zaɓi wanda zai zama mataimaki ba, Hadimi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Atiku ya lashe zaben fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa bayan ya lallasa Gwamna Wike na Ribas, Sanata Bukola Saraki da sauran yan takara ranar Asabar a Abuja.

Bayan kammala taron cikin nasara, hankalin jam'iyyar PDP kacokan ya koma kan wanda zata zaƙulo su yi takara tare da Atiku daga kudancin Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Batun dai ya kai ga samun rabuwar kai tsakanin kwamitin gudanarwa NWC da kwamitin amintattu BoT, kowa ya ce a shirye yake ya taimaka wa Atiku ya ɗauki wanda zai taka rawa wajen samun nasara a 2023.

Yaushe ake tsammanin fitar da mataimakin?

Da yake martani kan cigaban, hadimin Atiku, Mista Ibe ya ce:

"Idan lokacin yin magana kan abokin takarar ya yi ba sai an dinga yaɗa ƙanzon kurege ba zamu fito mu bayyana wa duniya. Ba zai zama wani abun yaɗawa a kafafen sada zumunta, Intanet da Whatsapp ba."

Kara karanta wannan

Gwamna ya faɗi wanda APC zata tsayar shugaban kasa idan har tana son cigaba da mulki a 2023

"Sabida haka daga bangarena iya abinda na sani ba zan iya tabbatar da gaskiyar labarin ba, yanzu lokaci ne na yaɗa jita-jita. Ya kamata mutane su yi hakuri su saurarin sanarwa a hukumance."

A wani labarin kuma Rikici ya ɓarke a Sakatariyar APC ta Abuja bayan ɗan takarar shugaban kasa ya jefa kyautar N50,000

Danbarwa ta barke tsakanin direbobi, jami'an tsaro da masoyan APC bayan gwamna Umahi ya watsa kyautar N50,000 a Abuja.

Bayanai sun bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasan ya watsa kudin ne yayin da yake gab da shiga Mota a Sakatariyar APC ta ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel