Shugabanci a 2023: Obasanjo na bakin ciki da yadda Atiku ya samu tikitin takara a PDP, yana shirya masa tuggu
- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, baya goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar
- Obasanjo bai ji dadin samun tikitin takarar jam’iyyar adawar da Atiku wanda yake dan arewa ya yi ba
- Tsohon shugaban kasar wanda ya so dan kudu ya gaji Buhari a 2023 yana duba yiwuwar marawa Peter Obi na jam’iyyar LP baya a zaben
Akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa sakamakon zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), bai yiwa wasu manyan shugabannin kudancin kasar dadi ba.
Daga cikin wadanda basu tsammaci sakamakon zai zo a haka ba harda tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.
Legit.ng ta dai kawo cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ne ya lashe zaben fidda gwanin bayan ya samu kuri’u 371, inda babban abokin hamayyarsa kuma gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya samu kuri’u 237.
New Telegraph ta rahoto daga wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta cewa tsohon shugaban kasar mara kabilanci, Obasanjo yana ganin cewa kamata yayi a mika shugabancin kasar na 2023 zuwa yankin kudu saboda daidaito, adalci da gaskiya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An tattaro cewa tsohon shugaban kasar na iya yanke shawarar marawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Mista Peter Obi baya.
Har zuwa lokacin da ya sauya sheka daga PDP, Obi wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Anambra yana sahun gaba a masu neman takarar shugabancin kasar a babbar jam’iyyar mai adawa a kasar.
Daya daga cikin majiyoyin ta ce:
“Bari na sanar da ku cewa Cif Obasanjo ya marawa Peter Obi baya ne saboda kishin kasa da kuma bukatar yin daidaito da adalci bisa la’akari da yanayin Najeriya.”
Binciken ya kuma nuna cewa wani tsohon gwamnan jihar Cross River da aka sakaya sunansa na nan yana nemawa Obi goyon baya bisa umurnin tsohon shugaban kasar.
Jaridar ta kuma nakalto majiyar na cewa:
“A ranar 29 ga watan Mayu, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya nuna rashin jin dadinsa game da sakamakon zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP.
“An yi zargin ya ba wani tsohon gwamnan jihar Cross River umurnin kaddamar da shirin marawa shugabancin kudu baya, inda hankali ya fi karkata ga zabar Obi.
“A zahirin gaskiya, an umurci tsohon gwamnan da ya hado kan Obi da jiga-jigan PDP da dama da suka fusata.
“Ya bayar da tabbacin jajircewa kan aikin tabbatar da ganin an cimma nasarar samun shugaban kasa dan kudu, saboda yin adalci da daidaito.
“Na san da batun cewa tsohon shugaban kasar ya ce zai tafi wajen kasar, sannan cewa idan ya dawo, zai hadu da masu dabarun, ciki harda tsohon gwamnan na Anambra.
“Obi ya yi farin ciki da goyon bayan, kuma ya yiwa tsohon shugaban kasar alkawarin jajircewa don cimma kasa mai cike da hadin kai, zaman lafiya da ci gaba.”
A ruwayar Leadershi, ta ce Donald Duk na kokarin nemawa Obi goyon baya inda tuni ya tuntubi wani jigo a jihar Cross River, yana nuna masa illar ci gaba da kasancewar mulki a arewa da kuma ware yankin kudu maso gabas da kudu maso kudu, wanda aka yi zargin an shirya a kasafin mulkin PDP.
Jerin sunayen 'yan takara 5 da ake sa ran Buhari zai zabi daya don ya gaje shi
A wani labarin, a ranar Talata, 31 ga watan Mayu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wani jawabi wanda ke ci gaba da haddasa cece-kuce, ya ce zai so ya zabi wanda yake so ya gaje shi gabannin zaben 2023.
Har zuwa lokacin da ya yi jawabin na ranar Talata, yan takarar kujerar shugaban kasar na APC wadanda suka fi 20 suna ta zuba idanu don zuwan ranar zaben fidda gwani wanda aka shirya yi a ranar 6 ga watan Yuni.
Sai dai kuma, tsarin ya sauya a yanzu domin shugaba Buhari ya bukaci gwamnonin APC su taimaka masa da aikin zabar wanda suke ganin ya kamata ya gaje shi.
Asali: Legit.ng