Gaskiyar magana: Jigo ya yi karin-haske a kan sauya-shekar Tinubu daga APC zuwa SDP
- Segun Oni ya yi magana a kan jita-jitar da ke yawo na sauya shekar Asiwaju Bola Tinubu zuwa SDP
- ‘Dan siyasar yana ganin cewa rade-radin bai tabbata ba, amma ya ce kofar jam’iyyarsu a bude ta ke
- Oni wanda tsohon jigo ne a APC ya nuna jam’iyyar SDP za ta tafi da kowa, ta kuma yi masu adalci
Abuja - A ranar Laraba, 1 ga watan Yuni, 2022, aka rahoto tsohon gwamnan jihar Ekiti, Segun Oni yana magana game da sauya-shekar Bola Tinubu.
Segun Oni ya nuna cewa babu abin da ke nuna tabbas Bola Tinubu zai shiga jam’iyyar hamayyarsu Social Democratic Party da aka fi sani da SDP.
Rahoton da Daily Trust ta fitar ya ce Oni ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa wasu tambayoyin da menama labarai suka yi masa jiya a Abuja.
‘Yan jarida sun nemi jin gaskiyar jita-jitar cewa Tinuu zai yi watsi da APC, ya shiga SDP muddin bai samu tikitin takarar shugaban kasa na zaben 2023 ba.
Har ila yau, an rahoto Oni yana mai cewa babu wani rikicin cikin gida a SDP, don haka tsohon gwamnan ya ce babu rabuwar kan da aka samu a jam’iyyar.
A ra’ayin fitaccen ‘dan siyasar, rade-radi kurum ake ji a kan batun Tinubu, ba abin da ya tabbata ba, amma ya nuna su na maraba da duk mai son cigaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kofar mu a bude ta ke - SDP
‘Dan takaran na gwamnan jihar Ekiti a zabe mai zuwa ya nuna cewa duk da haka kofar jam’iyyar SDP a bude ta ke, ta karbi masu irin akidu da manufarta.
Tsohon jigon na jam’iyyar APC mai mulki ya fadawa manema labarai cewa SDP za ta karbi duk wanda zai gyara damukaradiyya, ya kawo shugabanci nagari
“Rade-radi sun yi yawa! Bari in fada maku, mu ‘yan jam’iyyar SDP ne. Abin da mu ka sani shi ne, kofar mu a bude ta ke ga kowa.”
“Ba mu toshe wata kafa a siyasa, za mu saurara. Sannan za mu dauki komai ba tare da nuna fifiko ba. A daina yawan daukar jita-jita.”
“Za mu shirya zaben ‘yan takara, a abin da mu ka sani, ba za a tsuke kofar tattaunawa da maslaha ba, za mu yi yadda za a dauki darasi.”
- Segun Oni
Dazu aka ji Tinubu Support Organisation da Northern Young Professionals for Tinubu sun ce Bola Tinubu ya kamata jam’iyyar APC ta ba takara a zaben 2023.
Ita ma kungiyar Disciples of Jagaban ta ce ja da Atiku Abubakar sai Tinubu, idan ba haka magoya baya sun hango rushewar APC a zaben shekara mai zuwa.
Asali: Legit.ng