Jam’iyyar NNPP ta dura zauren Majalisar Dattawa, Sanatan Bauchi ya yi watsi da APC
Bisa dukkan alamu Lawan Yahaya Gumau ya tattara kayan shi, ya hakura da zama a jam’iyyar APC
An ga Sanata Lawan Yahaya Gumau dauke da fam na takarar ‘dan majalisar dattawa a jam’iyyar NNPP
Gumau yana cikin wadanda APC ta hana tikitin tazarce, amma bai cire ran komawa majalisa a 2023 ba
Bauchi - Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Sanata Lawan Yahaya Gumau ya fita daga jam’iyyar APC mai mulki, ya sauya-sheka ne zuwa NNPP.
Saifullahi Muhammad Hassan, daya daga cikin Hadiman jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso ne ya tabbatar da wannan labarin.
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa, Malam Saifullahi Hassan ya tabbatar da cewa Lawan Yahaya Gumau ya shiga jam’iyya mai kayan marmari.
Bayan ya fice daga APC mai mulkin Najeriya da rinjaye a majalisar dattawa, Sanatan bai yi wata-wata ba, ya yanki fam a jam’iyyar hamayyar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jawabin da Hassan ya fitar a ranar Laraba, 1 ga watan Yuni 2022, ya nuna Sanatan na kudancin Bauchi ya yanki fam din neman Sanata a NNPP.
APC ta hana Gumau takara
Sanata Gumau ya cin ma wannan mataki ne ganin cewa ya sha kasa a zaben tsaida ‘yan takarar Sanata da jam’iyyar APC ta shiya a jihar Bauchi.
Gumau yana cikin ‘yan majalisa masu-ci da ba za su iya samun nasara a zaben tsaida gwani ba.
A hotunan da ke yawo, an ga Sanatan tare da Rabiu Kwankwaso da wasu mabiya darikar Kwankwasiyya rike da takardun shiga zabe a NNPP.
Gumau ya yi shekara 4 a Majalisa
‘Dan majalisar mai shekara 51 a Duniya ya zama Sanata ne a 2018, bayan rasuwar Sanata Isa Wakili, kafin na ‘dan majalisa ne na mazabar Toro.
Idan za a tuna Gumau ya samu gagarumar nasara a zaben cike gurbin da INEC ta gudanar, ya doke ‘dan takarar PDP a yankin kudancin jihar Bauchi.
Babu mamaki wasu daga cikin Sanatocin jihohin Arewa su dauki wannan salo, su sauya-sheka ganin jam’iyyunsu sun hana su damar zarcewa a ofis.
An yi bari a Bauchi
A rahoton da mu ka fitar, kun ji yadda duka Sanatoci uku da ke kan mulki su ka sha kasa a zaben fitar da gwanin jam’iyyar APC da aka shirya a Bauchi.
Muhammad Adamu Bulkachuwa ya yi mummunar faduwa a zaben, ya kare babu ko kuri'a daya. Shi ma Halliru Jika ya gagara samun takarar gwamna.
Asali: Legit.ng