2023: Kar ku ɗauka kwace mulki hannun APC abu ne mai sauki, Atiku ga PDP

2023: Kar ku ɗauka kwace mulki hannun APC abu ne mai sauki, Atiku ga PDP

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya gargaɗi mambobin PDP su tashi tsaye kar su ɗauka faɗuwar APC abu ne mai sauki
  • Bayan karban shaidar zama ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku ya ce akwai ɗanyen jan aiki a gaban kowane mamba a PDP
  • Ya bayyana tsantsar jin daɗinsa na samun damar sake rike tutar PDP a zaɓen da ke tafe

Abuja - Ɗan takarar PDP a zaɓen 2024l3 dake tafe, Alhaji Atiku Abubakar, ya gargaɗi mambobin jam'iyya da su koma aiki gadan-gadan kar su ɗauka, "rashin nasara da ke gaba," ga APC mai mulki abu ne mai sauki.

Da yake jawabi ga mambobin kwamitin gudanarwa NWC, jiga-jigan PDP, da masoya jim kaɗan bayan karban shaidar takarar shugaban kasa, Atiku yace abun da ya faru ba zaɓe bane illa matakin tunkarar babban zaɓe.

Kara karanta wannan

Rudani: Sabbin bayanai sun fito, yayin da gwamnonin APC ke shawari kan zaban magajin Buhari

Atiku a wurin karɓam shaidar takara.
2023: Kar ku ɗauka kwace mulki hannun APC abu ne mai sauki, Atiku ga PDP Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Ɗon haka, tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya roki kwamitin NWC da ya jawo kowa a jiki domin kwace ragamar mulki daga hannun APC, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Atiku ya ƙara da cewa, "Kar mu yi kuskuren ɗauka rashin nasarar su abu ne mai sauki, wajibi mu haɗa kai, mu yi aiki tuƙuru kan kowace kuri'a. Akwai babban aiki a gaban mu, bamu da lokacin ɓatawa, kawai mu kama aiki."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Na yi farin ciki da sake samun wannan damar - Atiku

Atiku ya ƙara da cewa ya yi murna matuka da samun damar rike turar PDP, "Ya kamata mu tuna cewa abun da ya faru yar fafatawa ce kawai a cikin gida don cimma matsaya ta yadda zamu tunkari gaba."

"Babbar fafatawar ita ce zamu kawo wa jam'iyya nasarar kujera lamba ɗaya a ƙasar nan. Yana bukatar baki ɗaya ƴaƴan PDP, masoya da masu fatan Alkairi, dole mu haɗa kan kowa da kowa."

Kara karanta wannan

Almundahanan Akanta Janar N80bn: Duk laifin Buhari ne, Buba Galadima

"Ba wanda zamu bari a gefe, na riga na ziyarci yan takarar da muka fafata tare a wata hanyar da zata kai mu ga dunkule wa wuri ɗaya mu fuskanci abokan hamayya, mu lallasa su a zaɓe, kana mu fara aikin ceto ƙasar mu."

A wani labarin kuma Bayan canza zaɓe, Ɗan tsohon gwamna ya lallasa tsohon shugaban FCC, ya lashe tikitin takarar gwamna a 2023

Ɗan tsohon gwamnan Kwara da Allah ya yi wa rasuwa, Hakeem Lawal, ya lashe zaɓen fidda gwanin SDP na takarar gwamna.

A zaɓen wanda aka canza, Hakeem ya samu kuri'u 606, ya lallasa tsohon shugaban FCC ta ƙasa, Mista Oba, mai kuri'u 177.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262