Takara a 2023: 'Haka Allah ya so' Gwamna Wike ya nemi masoyansa su kwantar da hankali

Takara a 2023: 'Haka Allah ya so' Gwamna Wike ya nemi masoyansa su kwantar da hankali

  • Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya nuna rashin jin daɗinsa da matakin barin Tambuwal ya sake jawabi har ya janye wa Atiku
  • A cewar Wike, bayan ya gama jawabinsa duk bai san da janyewa ba, sai dai kaunarsa ga PDP ta sa ya zuba wa zuciyarsa ruwan sanyi
  • Ya kara da cewa duk da bai samu nasara ba, amma yana da kwarin guiwar ya ɗaga martabar siyasar jahar Ribas

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana yadda ya kusa ta da yamutsi filin taron zaɓen fid da gwanin PDP na takarar shugaban kasa yayin da ya nemi magoya bayansa sun kwantar da hankali.

Gwamnan ya yi jawabi ne a wurin liyafar da aka shirya domin girmama shi ranar Litinin a fadar gwamnati da ke Patakwal bayan dawo wa daga Abuja, kamar Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Atiku ya sa labule da Gwamna Wike bayan lallasa shi a zaɓen fid da gwanin PDP

Gwamna Wike na Ribas.
Takara a 2023: 'Haka Allah ya so' Gwamna Wike ya nemi masoyansa su kwantar da hankali Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wike ya ce ya yi yunkurin hana cigaban zaɓen lokacin da ɗan takara, wanda ya gama jawabinsa tun farko, aka ba shi dama ya dawo ya sanar da janyewarsa, hakan ya saɓa wa dokokin zaɓen.

Wike ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ban taɓa ganin yadda mutane zasu karya doka da ƙa'idojin da aka kafa ba, wani da ya gama jawabinsa, a wannan lokacin zai janye idan yana da burin haka. Bai kamata ku sake kiran shi ya dawo ba."

Da yake magana kan dalilin da yasa zuciyar ta yi sanyi gwamnan ya ce, "Sai na faɗa wa kaina, bai kamata a tarwatsa jam'iyyar mu ba."

Haka Allah ya tsara inji Wike

Gwamnan ya kuma yi kira da masoyansa su kwantar da hankulansu, inda ya kwatanta rashin nasarar da ya samu da haka Allah ya tsara.

Kara karanta wannan

Kala-Balge: Zulum ya kai ziyarar jaje ga iyalan mutane 30 da aka yanka a Borno

"Haka Allah ya so, don haka kada mu sa damuwa a zuƙatan mu," a cewar Wike yayin da ya caccaki gwamnonin kusu da yaudara.

"Shiyasa aka bar mu a baya wajen cigaba, duba yadda yan ɗaya yankin suka haɗa kan su wuri ɗaya, amma mu nan ko tunanin haka ba mu yi ba."
"Mutum ya zama sanadin amfani da shi a yaƙi abinda mutanensa suke so kuma yana tunani ya yi nasara, ta ina ya dai ji kunya."

Gwamnan ya ce duk da bai samu nasara ba amma yadda ya yi kokari a zaɓen ya ɗaga martabar siyasar jihar Ribas da kuma sauran kananan kabilu.

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta tantance gwamnan Jigawa, Tinubu da Amaechi sun dira wurin a Abuja

Kwamitin da APC ta kafa domin tantance duk kan yan takararta, wanda ke karkashin Jonh Oyegun na cigaba da aiki gadan-gadan.

Jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu, da tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, sun isa wurin da yammacin nan na ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana a kan zargin yi wa Wike ko wani ‘dan takara aikin boye a PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel