2023: Jerin sunayen yan takarar APC da PDP 29 da suka mallaki tikiti ba tare da hamayya ba

2023: Jerin sunayen yan takarar APC da PDP 29 da suka mallaki tikiti ba tare da hamayya ba

Kamar yadda muka sani an fitar da sakamakon zabukan fidda gwani na gwamnoni, sanatoci, yan majalisar wakilai da na yan majalisar jiha na jam’iyyun APC da PDP.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abun sha'awa wasu yan takarar jam’iyyun biyu sun mallaki tikitin takara ba tare da hamayya ba ga dukkan alamu kuma sun zage damtse don ganin sun yi nasarar darewa kujerun da suke muradi tun kafin zaben na 2023.

2023: Jerin sunayen yan takarar APC da PDP 29 da suka mallaki tikiti ba tare da hamayya ba
2023: Jerin sunayen yan takarar APC da PDP 29 da suka mallaki tikiti ba tare da hamayya ba Hoto: @AhmaduFintiri, @BuniMedia, @ProfZulum, @Bellomatawalle1
Asali: Twitter

A wannan zaure Legit.ng ta tattaro jerin sunayen yan takara daga PDP da APC wadanda suka samu tikitin takara a jihohinsu daban-daban a lokacin zaben fidda gwani ba tare da karawa da kowa ba.

 1. Gwamna Bello Matawalle (Zamfara, APC)
 2. Gwamna Babagana Zulum (Borno, APC)
 3. Gwamna Muhammed Inuwa (Gombe, APC)
 4. Sa’idu Umar (Zaben gwamnan Sokoto, PDP)
 5. Mai Mala Buni (Yobe, APC)
 6. Ibrahim Kassim (Zaben gwamnan Bauchi PDP)
 7. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri (Adamawa PDP)
 8. Gwamna AbdulRahman Abdulrasaq (Kwara APC)
 9. Uche Nnaji (Zaben gwamnan Enugu, APC)
 10. Ovie Omo-Agege (Zaben gwamnan Delta, APC)
 11. Peter Nwaoboshi (Sanata mai wakiltan Delta ta arewa, APC)
 12. Ede Dafinone (Sanata mai wakiltan Delta ta tsakiya, APC)
 13. Joel-Onowakpo Thomas (Sanata mai wakiltan Delta ta kudu, APC)
 14. Bolaji Abdullahi (Sanata mai wakilta Kwara ta tsakiya, PDP)
 15. Rafiu Ibrahim (Sanata mai wakiltan Kwara ta kudu, PDP)
 16. Bala Mande (Sanata mai wakiltan Zamfara ta arewa, PDP)
 17. Desmond Elliot (Mazabar. Surulere I a Lagos, APC)
 18. Femi Gbajabiamila (Kakakin majalisa, mazabar Surulere I a Lagos, APC)
 19. Tokunbo Abiru (Sanata mai wakiltan Lagos ta gabas, APC)
 20. Opeyemi Bamidele (Sanata mai wakiltan Ekiti ta tsakiya, APC)
 21. Tanko Al-Makura (Sanata mai wakiltan Nasarawa ta kudu, APC)
 22. Abdul’aziz Yari (Sanata mai wakiltan Zamfara ta yamma, APC)
 23. Kabiru Marafa (Sanata mai wakiltan Zamfara ta tsakiya, APC)
 24. Aliyu Wamakko (Sanata mai wakiltan Sokoto ta tsakiya APC)
 25. Ahmad Kaita (Sanata mai wakitan Katsina ta arewa PDP)
 26. Orji Uzor Kalu (Sanata mai wakiltan Abia ta arewa, APC)
 27. Adams Oshiomhole (Sanata mai wakiltan Edo ta arewa, APC)
 28. Kabiru Gaya (Sanata mai wakiltan Kano ta kudu, APC)
 29. Barau Jibrin (Sanata mai wakiltan Kano ta arewa, APC)

Kara karanta wannan

Rochas Okorocha, Lawan da sauran yan takarar shugaban ƙasa 9 da Kwamitin APC zai tantance yau

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan Borno a 2023: Dan takarar PDP ya zargi Zulum da son kai, ya sha alwashin tsige sa daga mulki

A wani labarin, dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic party (PDP) a zaben gwamnan jihar Borno na 2023, Mohammed Jajare, ya zargi gwamnan jihar, Babagana Zulum na baiwa abokai, iyalai da yan uwansa kwangiloli ta hanyar fakewa da aiki kai tsaye.

Jajare ya kuma yi zargin cewa gwamnan na siye manyan yan PDP a jihar don kawar da adawa a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel