Gaskiya ta Fito: Abin da Tambuwal ya faɗa wa shugaban PDP da wasu yan takara biyu kafin janye wa Atiku
- Wasu bayanai da suka fito sun bayyana yadda Tambuwal ya nemi shawarin shugaban PDP da wasu mutum biyu kafin janye wa Atiku
- Wata majiya ta ce gwamnan ya faɗa wa Bukola Saraki, Bala Muhammed, matakin da ya ɗauka kafin zuwa wurin Ayu
- Matakin janyewar Tambuwal ta taka rawar gani wajen nasarar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku ya samu
Abuja - A ranar Lahadi, shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya bayyana gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, da gwarzon zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa da aka kammala.
Mista Ayu ya yaba masa yayin da yake tsokaci kan janyewar da ya yi wa Atiku yayin zaɓen, cigaban da yake ganin shi ya ceto PDP daga ƙara zafin takara tsakanin mutum biyu.
Jaridar Premium Times ta samu wasu bayanai kan matakin gwamna Tambuwal yan daƙiƙu ƙaɗan kafin ya fito munbari ya sanar da janyewa Atiku.
Bincike ya nuna cewa Ayu na ɗaya daga cikin mutum uku da Gwamnan ya nemi shawarin su kafin sanar da abin da zuciyarsa ta yanke.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tambuwal, kamar kowane ɗan takara ya yi amfani da Mintuna biyar ɗinsa wajen jawo hankalin Deleget da rokon su kaɗa masa kuri'a a zaɓen da za'a fara.
Yadda Tambuwal ya nemi shawarin mutum uku
Bayan ɗan takara na karshe ya gama jawabinsa, ba zato Tambuwal ya tashi, ya kira wani tsohon gwamna suka tafi tare zuwa wurin gwamna Bala Muhammed na Bauchi, inda ya sanar masa zai janye wa Atiku.
A cewar wani jigon PDP da ya halarci wurin, Kauran Bauchi ya nuna mamakinsa ƙarara kafin daga bisani ya nemi jin dalilin ɗaukar matakin daga takwaransa gwamna.
Majiyar ta ce Muhammed ya yi kokarin canza wa Tambuwal tunaninsa, amma daga ƙarshe ya shaida masa ya riga ya yanke hukunci a zuciyarsa ba zai canza ba.
Bayan nan, gwamna Tambuwal ya nufi wurin da tsohon gwamnan Kwara, Bukola Saraki, ke zaune ya faɗa masa irin abin da ya gaya wa Kauran Bauchi.
Majiyar ta ce nan take fuskar Saraki ta canza zuwa mamaki, daga baya ya tuna masa cewa sun yi yarjejeniya tsakanin su wani ya janye wa wani, yana nufin kamata ya yi Tambuwal ya janye masa.
Ya ce:
"Amma tambuwal ya ba shi amsar cewa babu wannan maganar yarjejeniya dan ba su yi haka ba, kuma ya duba duk wasu abubuwa kafin yanke janye wa daga burinsa ya koma bayan Atiku."
Daga nan wurin Saraki, Tambuwal ya nufi kujerar da shugaban PDP ke zaune, majiyar ta ƙara da cewa:
"Ya je ya gaya wa shugaban PDP cewa zai janye kuma ya faɗa wa abokan takararsa (Saraki da Muhammed) matakin da ya ɗauka."
Ayu ya kara wa gwamnan kwarin guiwa kafin daga bisani shugaban kwamitin taron ya sanar da cewa gwamna Tambuwal na da muhimmin saƙon da zai isar kafin fara kaɗa kuri'a.
Jihohin da Tambuwal ke da goyon baya
Daga nan Tambuwal ya sake komawa kan Mumbari ya sanar da janyewa daga tseren takara, inda ya ce ya ɗauki matakin ne saboda fifita jam'iyya da ƙasa.
Kafin janyewarsa, Bayanai sun nuna cewa Tambuwal ke da goyon bayan shugabanni da Deleget a jihohi 6 daga cikin Bakwai na arewa ta yamma da Imo, Nasarawa, Anambra, Kogi, Ondo da Benuwai.
A wani labarin na daban kuma Hukumar EFCC ta ayyana neman wani tsohon ɗan majalisar tarayya ruwa a jallo, ta nemi a cafke shi
Hukumar EFCC ta ayyana neman tsohon ɗan majalisar tarayya ruwa a jallo bisa wasu dalilai guda biyu.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, EFCC ta ce Mista Nzeribe, ya tsallake sharuddan beli da kotu ta ba shi kuma ya daina halartar shari'a.
Asali: Legit.ng