Tashin hankali: Cikin 'yan tawagar Tinubu ya duri ruwa, yayin da ake ci gaba da tantance 'yan takara

Tashin hankali: Cikin 'yan tawagar Tinubu ya duri ruwa, yayin da ake ci gaba da tantance 'yan takara

  • Cikin magoya bayan babban jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu wajen neman tikitin shugaban kasa na jam'iyyar a zabe mai zuwa ya duri ruwa
  • Hakan ya kasance ne saboda bayyanar tsohon shugaban jam'iyyar, Cif John Odigie-Oyegun a matsayin shugaban kwamitin tantance masu neman takara
  • An dade ba a ga maciji tsakanin Oyegun da babban jagoran na PDP tun a lokacin zaben gwamnan jihar Edo na 2020

Abuja - Ana zaman zullumi a sansanin siyasar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, yayin da Cif John Odigie-Oyegun ke jagorantar kwamitin tantance masu neman masu neman takara.

Ana ganin akwai takun saka tsakanin Odigie-Oyegun, tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa da babban jagoran jam’iyyar na kasa tun a lokacin zaben gwamnan jihar Edo na 2020.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta tantance gwamnan Jigawa, Tinubu da Amaechi sun dira wurin a Abuja

Oyegun ne ke jagorantar kwamitin mutum bakwai don tantance masu neman takarar shugaban kasa na APC a yau Litinin a Abuja gabannin taron jam’iyyar, jaridar Punch ta rahoto.

Tashin hankali: Cikin 'yan tawagar Tinubu ya duri ruwa, yayin da ake ci gaba da tantance 'yan takara
Tashin hankali: Cikin 'yan tawagar Tinubu ya duri ruwa, yayin da ake ci gaba da tantance 'yan takara Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A yayin zaben, Fasto Ize-Iyamu, wanda ke da goyon bayan Tinubu ya sha kaye a hannun Gwamna Godwin Obaseki mai ci, duk da ya sauya sheka zuwa Peoples Democratic Party (PDP).

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yan siyasa a sansanin Tinubu sun yi zargin cewa Oyegun ya ci dunduniyar jam’iyyar don tabbatar da nasarar Obaseki.

Sun nuna tsoron cewa Oyegun na iya marawa dan takara mara karfi baya don PDP ta sake komawa kan mulki.

Daya daga cikin shugaban kungiyar magoya bayan Tinubu ya ce:

“Akwai tsoro da fargaba a tsakanin masu takarar da kuma sansanoni daban-daban saboda Cif Oyegun ya zama mai kawo cece-kuce da rigima a jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen sanatoci 42 da ba lallai su koma majalisar dattawa ba a 2023

“Yana daga cikin wadanda suka kitsa tsige Adams Oshiomhole da korar tsohon kwamitin NWC. Ya marawa Obaseki baya a zaben da APC ke da dan takarar gwamna a jihar Edo. Batun da ke yi a yanzu shine ko Cif Oyegun ba zai yi son kai ba.”

Wani magoyin bayan Tinubu ya ce:

“Ya za a ce sai Oyegun a cikin dukka mutane? Ta yaya zai zama dan jam’iyyar tsaka-tsaki a wannan batu? Duk mun san rawar ganin da Tinubu ya taka wajen tsige Oyegun da kuma abun da Oyegun ya aikata a zaben Edo na karshe. Ina fatan ba zai yi son kai ba.”

Babu Jonathan: Jerin sunayen yan takarar shugaban kasa 23 da APC za ta tantance

A gefe guda, babu sunan tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan a jerin masu neman takarar shugaban kasa da ake sanya ran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za ta tantance.

Kara karanta wannan

Tsohon dan takara a PDP ya lashe tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour

A watan Afrilu ne magoya bayansa suka yiwa gidansa na Abuja tsinke inda suka nemi ya tsaya takarar shugaban kasa na 2023, amma Jonathan bai yi martani ba.

Yan kwanaki bayan nan, wata kungiya ta Arewa ta siya masa fom din takara ta APC amma tsohon shugaban kasar ya karyata amincewa da siya masa fom din.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng